Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Kwamitin Da Amaechi Ya Kafa Ya Wanke Hadiza Bala Usman Daga Badakalar Kudi A NPA

Daga Bello Hamza, Abuja Kwamitin mutum 11 da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya kafa don bincikar Shugabar Hukumar Tashoshin Ji...


Daga Bello Hamza, Abuja

Kwamitin mutum 11 da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya kafa don bincikar Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) da aka dakatar, Hadiza Bala Usman, ya wanke ta daga dukkan zargen-zargen da aka yi mata na hannu a badakalar karkatar da kudaden hukumar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya dakatar da Hajiya Hadiza Bala Usman a kan zargin rashin mika Naira Biliyan 165 na rarar kudaden shigar hukumar zuwa asusun gwamnatin tarayya, abin kuma da ta musanta aikatawa.

Wani bangare na rahoton da jaridar DAILY NIGERIAN ta gani ya nuna cewa, kwamitin bai samu Hajiya Hadiza Bala Usman da wani laifi ba a kan abin da ya shafi rashin mika Naira Biliyan 165 ga asusun gwamnatin tarayya.

A ranar 10 ga watan Janairu ne kwamitin ya mika rahotonsa bayan wata 8 ya na zama da kuma jinkiri don ganin an kawo cikas a kan umarnin shugaban kasa na a dawo da ita bakin aikinta.

Aikin da aka dora wa kwamitin sun hada da gudanar da bincike don sanin hanyoyi da dabarun da shugabar hukumar NPA ta yi amfani dasu, sun kuma gano cewa, dukkan hanyoyin da ta yi amfani dasu sun yi daidai da dokokin hukumar da aka kafa tun shekarar 2016 zuwa yanzu.

”Ku duba tare da bincikar yadda aka dakatar da wasu manyan kwangiloli a NPA a kuma tabbatar da cewa, ko wannan mataki ya yi daidai da hukunce-hukunce kotu da kuma umarnin Shugaban Kasa; a kuma duba tare da bincikar ko hanyoyin da aka aiwatar da lamarin ya yi daidai da ka’ida da dokokin da ke tafiyar da ma’aikatun gwamanatin tarayya; a duba tare da bincikar ko sun yi daidai da dokokin aiwatar da kwangila na gwamnati da aka kafa tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu,” wannan wasu ne daga cikin ka’idar aikin da aka ba kwamitin.

Duk da cewa, ba akai ga bayyana wa al’umma cikakken sakamakon da ke kunshe a rahoton kwamitin ba, amma Jaridar Daily Nijeriya ta nakalto cewa, kwamitin ya tabbatar da cewa, Hajiya Hadiza Bala Usman ta zuba Naira Biliyan 182.99 cikin asusun tattara kudaden shiga na kasa, ‘CRF’.

Rahoton ya ce, “NPA ta bayar da cikakken bayanai na yadda ta mika rarar kudaden da aka samu a hukumar, wanda ake kira da ‘Operating Surplus Payments, CRF’ zawa asusun gwamnatin tarayya, kuma ofishin ma’ajin gwamnatin tarayya ya tabbatar da karbar kudaden,”

Rahoton ya kuma kara da cewa.

“Bayani a kan matsayin NPA, duba da wasikar da ta fito daga Ofishin Tsara Kasafin Kudi na Gwamnatin Tarayya, sun bayyana ra’ayin su karara na cewa:- ‘…Aiwatar da kasafin kudi ba zai zama wani ma’auni na karshe ba na yanke hukuncin yadda aka aiwatar da rarar kudade ba saboda…..Jadawalin da aka tantance ne kawai ma’aunin da za a iya amfani dashi, wannan kuma haka ake yi a fadin duniya ….. in aka yi la’akari da sashi na 22.2 da kuma na 23.3 na dokar tsare-tsaren tattalin arzikin kasa (FRA) na shekarar 2007…'” (Ann. BI)

Rahoton binciken ya mayar da hankali ne a kan dukkan zamanin shugabancin Hadiza a hukumar, inda suka tabbatar da cewa, bayan bin da suka yi daki-daki na alkalummar da suka fito daga NPA sun same su daidai da da abin daya fito daga ofishin Akanta Janar na Tarayya, OAGF.

“Aikin bicike da aka gudanar na hadin gwiwa da hukumar NPA tare da ofishin Akanta Janar na Tarayya daga shekarar 2016 zuwa watan Mayu na 2021 an bi diddigin dukkan kudin bayanai an kuma tabbatar da NPA ta bayar da dukkan kudaden da ake magana a kai ba tare da kwange ba. (wasikar ranar 30 ga watan Agusta 2021 daga ofishin Akanta Janar mai lamba R&I/021/B/367) (Ann. BII) ya tabbatar da haka.

“Daga watan Janairu na shekarar 2016 zuwa Mayu, 2021, hukumar NPA ta zuba Naira Biliyan 182.99 a assusun gwamnatin tarayya. Kwamitin ya tabbatar da haka ne ta bayanan da suka fito daga hukumar NPA, tare da shaidun rasitai daga karamin ofishin ma’aji na gwmanatin tarayya, sun tabbatar cewa, dukkan rarar kudaden sun shiga asusun gwamnatin kamar yadda wasikar Akanta Janar na Gwamnatin tarayya ya tabbatar wa kwamitin.

Duk da wanke Hadiza Bala Usman da kwamitin ya yi, Ministan Sufuri, Ameachi bata takardar gargadi, yana tuhumarta da ‘Tsananin rashin da’a’ a matsayin ta na Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya daga ranar 18 ga watan Yuli 2016 zuwa ranar 6 ga watan Mayu, yana mai umartanta da ta amsa tuhumar a cikin kwanaki 7.

Wasu daga cikin tuhumar da ke kunshe a cikin takardar sun hada zargin rashin biyayya ga umarnin Minista; sayan manyan motocin TTP, da aka shirya amfani dasu don shirin nan na ‘e-Call Up’;  da karya dokokin sadarwa tsakanin hukumoin gwamnati, da sayan wasu motocin gudanar da ayyuka, da sauran su.

A martanin data bayar, Hadiza Bala Usaman ta karyata zargn kin bin umarnin Minista, ta kuma yi bayani dalladalla a takarda mai shafi 23 da ta rubuta, inda ta tabbbatar cewa bata karya wata doka ba a matsayinta na shugabar hukumar NPA.

A martaninta kan kin bin umarnin Minista, ta bayyana cewa: “Hukumar kula da yadda ake sayen kaya na gwamnati BPP ta mayar da martani ta wasikar data rubuto ranar 18 ga watan Yuni 2020 (an hada da kwafin wasikar a matsayin shaida ta 2) a shadara ta 6, BPP ta lura da bukatar karin wa’adin shekara 1 da HMT ya nema ta kuma mika bukatar ga mahunkunta. A shadara ta 7 na wasikar BPP ta nuna cewa, za ta amince da karin wa’adin wata 6 ne kawai, don hukumar ta samu lokacin daidata lamarin don ya yi daidai da yadda ake yi a kasashen duniya. An kuma sanar da wannan matsayar ga HMT ta hanyar wasikar da aka rubuta a ranar 30 ga watan Yuni 2020, wasika mai lamba MD/10/FMT/BOL.DD/366, an kuma hada wasikar a matsayin shaida ta 2B.

“An kuma wallafa takardar sanarwa na soke lamarin a manyan jaridun Nijeriya 2 a ranar 8 ga watan Yuni 2020 an kuma sanya a jaridar ‘Federal Tenders Journal’. Wannan yana nuna cewa, ban taba kin bin umarnin MInista ba na kuma isar da bukatar haka ne ga BPP. Amma hukumar BPP ta ki amincewa da bukatar karin shekara 1 maimakon haka ta bayar da karin wata 6 don hukumar ta samu damar kammala shirye-shiryen daya kamata na bayar da kwangilar. Duk wani musayar sakonni da aka yi da BPP a kan karin wa’adin wata shida an an yi ne don cika ka’idar doka kamar yadda BPP ta umarta a wasikar da suka aiko a ranar 18 ga watan Yuni 2020.

“A kan maganar kin bin umarnin Mai Girma Minista na ranar 4 ga watan Mayu 2020, ina mai bayyana cewa, musayar wasikar da aka yi da BPP ba an yi ne don a kara sabon wa’adin sayen wasu kayyaki bane ko wasu bukatu da ke neman sai MTB ko FEC sun sani. Amma wani lamari ne da ba sai an samu sanya bakin MTB da FEC.  A kan haka ba a karya doka ko kuma kin bin umarnin Minista ba wadda ta ce, dole dukkan abubuwan da suka shafi saye da tallata ayyuka sun bi ta hannun kwamiti minista na ‘Ministerial Tenders Board (MTB)’, BPP ko kuma FEC kamar yadda wasikar da aka aiko ranar 4 ga watan Mayu 2020 ya bayyana.

“A kan wadanna bayanan na sama, ina mai bayyana cewa, ba a ki bin umarni ko kin aiwatar da umarnin Minista ba ko kadan.”

A kan yadda aka sayi motoci bayan da barnar da zanga-zangar EndSARS ya haifar wanda ya kai ga lalata kayayyakin jama’a, ciki har da babbar hedikwatar NPA da ke Legas, Mista Amaechi ya tuhumi hukumar NPA akan yadda suka sayi motoci na Naira Biliyan 1.277 don maye gurbin wadanda suka kone ba tare da amincewa majalisar zartasawa ta kasa ba.

A martaninta, Hadiza Baka Usman ta ce, “A ranar Laraba 21 ga watan Oktoba 2021 ‘yan ta’adda sun kai hari heikwatar NPA da ke Marina a Jihar Legas. Harin ya kai ga lalata babbar ginin hukumar, da wasu gine-gine da wajen ajiye motoci da cibiyar kashe gobara ta ma’aikatar da dai saransu. Bayan barnar da suka yi wa gine-ginen, sun kuma kona motocin aiki da kuma dukkan motoncin ma’aikata da aka ajye a warin ajiye motoci na ma’aikatan. Wasu motocin na daga cikin wadanda muke amfani dasu na yau da kullum, muna kuma amfani da wasu wajen tattara kudaden shiga. Wannan barnar da aka yi wa hukumar ya durkusar da ma’aikatar musamman abin da ya shafi tattara kudaden shiga da sauran gudanarwa. Don dakile asarar da ake tafkawa hukumar ta dauki aniyar samar da makwafinsu ta hanyar tsarin gaggawa wanda kuma shi ne hanya mafi tsari da yakamata mu bi a wannan lokacin.

“An yi sayayyen ne ta hanyar bin ka’idojin sashi na 43 (1) (a), (2), (3) and (4) na dokar sayaen kaya na gwamnatin tarayya na shekarar 2007 (PPA) kamar yadda muka kawo a kasa: 43-(1) “Za a iya yin sayayyan gaggawa kamar yadda wannan kudurin ya tanada;

“(a) Kasa na iya fuskantar wata tashin hanakali ko bala’i ko kuma yaki, amma kuma dukkan wadanda kaddara ne daga Allah;”

“(2) In aka fuskanci lamarin gaggawa, ana iya yin sayayyar kayyaki ko samar da aiki kai-tsaye. (3) duk siyayyar da aka yi karkashin lamari na gaggawa za’a dauke shi da muhimmanci tare da kuma bin dukkan ka’idojin da suka kamata tare da lura da irin matsalar gaggawar da ake fuskanta. (4) da zaran lamarin ya daidaita dole a samar da cikakken rahoto da za a mika wa BPP don sanya hannu tare da bayar da takardar shaidar “No Objection”. Ina mai jawo hankain ka a kan cewa, sayyayen gaggawar da aka yi an yi ne kamar yadda yake a sashi na 43-1, 2, 3 da 4 na dokokin PPA kamar yadda muka kawo a sama, ana ba hukumar shawarar da ta gaggauta ci gaba da sayayyen da za ta yi na gagauwa daga baya kuma ta samar da cikakken rahoto da kuma takardar shaidar “No Objection”.

No comments