Rfi ta labarto cewa 'yan bindiga sun kai samame wani sansanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma a garin Ishau, na karamar hukum...
Rfi ta labarto cewa 'yan bindiga sun kai samame wani sansanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma a garin Ishau, na karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja, inda suka kashe jami’a 3.
Jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a kasar ta ruwaito cewa ‘yan bindigar suna wucewa ne, inda suka yi kicibis da wata tawagar ‘yan sanda da ke sintiri, nan ne fa aka fara bai wa hammata iska a tsakaninsu.
Majiyoyi sun ce barayin dajin na barin jihar Neja ne zuwa Kaduna, sai suka yi amfani da damar wajen kaddamar da hare hare a kan al’ummomin da ke iyakokin jihohin biyu.
Kokarin samun karin bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar Nejar ya ci tura.
No comments