Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Yan Bindiga Sun Sace Mata Da 'Ya'yan Sarkin Hausawa A Jihar Kaduna

BBC ta labarto cewa; Barayin daji sun yi dirar mikiya a gidan Sarkin Hausawa na Anguwar Azara da ke garin Jere a kan hanyar Abuj...


BBC ta labarto cewa; Barayin daji sun yi dirar mikiya a gidan Sarkin Hausawa na Anguwar Azara da ke garin Jere a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Mallam Ibrahim Tanko, inda suka sace matansa da ‘ya’yansa mata hudu.

Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa a hirar da ta yi da shi inda ya tabbatar mata da labarin ya ce, barayin sun saki daya daga cikin matan nasa, mai suna Hauwau wadda ita ce uwar-gida, bayan da suka ga cewa tana fama da hawan jini.

Ya ce barayin wadanda suka farmaki gidan nasa ranar Talata, da muggan makamai sun je ne da misalin karfe 11:52 na dare.

Ya ce ya yi kokari ne ya gudu inda ya bi ta daya daga cikin kofofin fita na gidan.

Sarkin Hausawan ya kara da cewa bayan da barayin suka bincike gidan ne ba su ganshi ba, sai suka je dakin da ‘ya’yansa mata suke barci suka rutsa su da bindiga suka tafi da hudu daga cikinsu.

Sannan ya ce bayan da suka bar gidansa ne sai kuma suka shiga na wani makwabcinsa, inda can ma suka tafi da mutum hudu da suka hada da wata mace mai goyo.

Ya ce sun sassari mijin matar da adda, suka barci magashiyan, inda yanzu yana asibiti ana jinyarsa.

Sarkin ya sheda wa jaridar cewa bayan sa’a daya da barayin suka tafi da mutanen da suka sata, sai sojoji sukaje.

Rahoton ya ce, da aka tuntubi kakakin ‘yan sanda na jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige, ya ce ba su da labarin harin a lokacin.

No comments