YANZU-YANZU: Naziru Sarkin Waka Ya Bai Wa Ladin Cima Tallafin Miliyan BiyuMADOGARA ta labarto cewa; Naziru Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya yi alƙawarin bai wa Ladin Cima kyautar naira miliyan biyu domin ta kama sana'a, inda kuma ya yi alkawarin shi da ƴan uwansa za su ci gaba da ɗaukar ɗawainiyarta.

Kazalika kuma Nazirun ya yi alƙawarin bai wa jaruma Fati Slow Motion kyautar miliyan guda biyo bayan bidiyon caccakar da ta yi masa, inda ya ce maganganun da ta fada a kansa, Allah zai yi maganin wannan. 

Nazirun ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa da yammancin yau Lahadi 13 ga watan Fabarairun 2022 a shafinsa na Facebook

Duk waɗannan dai ya biyo bayan dambarwar da ake tafkawa a wannan makon a masana'antar finafinan Hausa ta Kannywood sakamakon furucin Ladin Cima na ƙarancin abin da ake ba ta a fim.

Ƙarin bayani zai zo nan gaba.

Post a Comment

0 Comments