YANZU-YANZU: Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Ta Cafke Abba Kyari


Rahotanni dake shigowa MADOGARA a halin yanzu daga Jaridar Punch  na nuni da cewa rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta cafke korarren dan sandan nan mai mukamin mataimakin Kwamishinan 'yan sandan Nijeriya, Abba Kyari. 

Jaridar ta labarto cewa an cafke shi ne tare da mutum hudu a yau Litinin. 

Kyari an kama shi ne awanni kadan bayan da Hukumar fatauci da yaki da miyagun kwayoyi ta Nijeriya, NDLEA, ta ayyana shi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bayan ya ki amsa gayyatarta bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi

Kazalika dai korarren dan sandan na kuma karkashin binciken Hukumar leken asiri ta Amurka wato FBI, bisa samunsa a cikin tuhumar da ake yi wa Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpupi bisa laifukan damfara da zambo. 

Post a Comment

0 Comments