Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Alƙalan Kotun Shari’ar Musulunci A Kano Sun Buƙaci Ganduje Ya Biya Su Kuɗin Rawani

Alƙalan Kotunan Shari'ar Muslunci a Jihar Kano sun roƙi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya taimaka ya biya su kuɗaɗen rawan...


Alƙalan Kotunan Shari'ar Muslunci a Jihar Kano sun roƙi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya taimaka ya biya su kuɗaɗen rawani.

Jaridar Kano Focus ta rawaito cewa Shugaban Kungiyar Alkalan Kotun Shari’ar Musulunci a jihar Kano, Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ne ya miƙa buƙatar ta su ga gwamnan.

Wannan dai wani ɓangare ne na alawus – alawus da ake biyan Alƙalai a Kano.

Sarki Yola, wanda shi ne alkalin babbar kotun shari’ar Musulunci da ke ƙofar Kudu a birnin Kano, ya ce alƙalai ba kamar sauran ma’aikata ba ne yana da kyau a riƙa kyautatu musu, wajen ganin an sauke nauyin biyansu haƙƙoƙinsu.

Ya kuma roƙi Gwamnan da ya biya su kuɗin Rawani na shekarar da ta gabata, domin karfafawa alƙalan gwiwa wajen gudanar da ayyukansu,

Ya ce akwai bukatar gwamnan  ya dubi ɓangaren su kasancewar ya yi umarni a biya su amma har yanzu kudin bai zo hannunsu.

No comments