Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ɗalibin Nijeriya Da Ya Guje Wa Yaƙi A Ukraine Ya Rasu A Sakkwato

Uzaifa Halilu Modachi, ɗalibi da ke karatu a Ukraine, ya rasu bayan kakanni biyu da dawo wa gida Sokoto bayan ya guje wa yakin d...


Uzaifa Halilu Modachi, ɗalibi da ke karatu a Ukraine, ya rasu bayan kakanni biyu da dawo wa gida Sokoto bayan ya guje wa yakin da Ukraine ɗin ke yi da Russia.

Rahotanni sun baiyana cewa, kafin dawowarsa gida Jihar Sokoto,  Modachi ya kai shekaru uku bai zo hutu ba da ga Ukraine, inda ya ke karatu aJami'ar Ilimin Lafiya ta Zaporozhye a ƙasar.

Mahaifin ɗalibin, Habibu Halliru Modachi, ya ce ɗan nasa, wanda ya ke a shekarar ƙarshe a jami'ar, ya rasu, kuma Allah ne Ya ga dama ya ɗauke shi.

A cewar mahaifin, wanda ɗan majalisar jiha ne, ya ce Allah ne Ya bashi ɗan kuma Ya karɓe abinsa.

Ya ƙara da cewa da Ukraine ɗin ɗan nasa ya rasu, da an fadi maganganu da dama cewa sojojin Russia sun kashe shi ko ma sojojin Ukraine sun kashe shi bisa rashin sani.

Bayan ya masa addu'a a kan Allah Hai masa Rahma, mahaifin ya kuma gode wa Allah da Ya sanya ya rasu a gaban iyayensa.

No comments