Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ƴan Bindiga Sun Kashe Ɗan Sanda A Batsari Ta Jihar Katsina

A ranar Litinin 28-03-2022, da rana tsaka wasu ƴan bindiga dake kan babur, ɗayansu na sanye da babbar riga (malum-malum) ɗaya ku...


A ranar Litinin 28-03-2022, da rana tsaka wasu ƴan bindiga dake kan babur, ɗayansu na sanye da babbar riga (malum-malum) ɗaya kuma ya sanya hijabi (abaya), suka kaima wani shingen jami'an tsaron ƴan sanda, dake ƙauyen Biya ta ƙaramar hukumar Batsari hari, inda nan take suka kashe ɗan sanda guda ɗaya, kuma ana tsammanin sun tafi da bindigar shi kamar yadda majiyar mu ta shaida mana. 

Wakilinmu a Batsari ya ji cewar ƴan bindigar sun koma ta hanyar da suka biyo, wacce ta bi kusa da gadar Gobirawa ta yi Yamma ta nufi Garin Runji.

Ƴan bindiga a Batsari sun bada wa'adin ƙwanaki bakwai na a yi sulhu da su ko su afka ma garin.

An dai riga an yi Jana'izar Marigayi Ahmed Shu'aibu Ƙwado da Misalin ƙarfe Uku na ranar a jiya Litinin a cikin Garin Katsina.

No comments