Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Gudanar Da Taron Sulhu Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Karamar Hukumar Guri

Daga Abubakar M. Taheer  An gudanar da taron sulhunta tsakanin manoma da makiyaya a a karamar hukumar Guri ta Jihar Jigawa wanda...


Daga Abubakar M. Taheer 

An gudanar da taron sulhunta tsakanin manoma da makiyaya a a karamar hukumar Guri ta Jihar Jigawa wanda ya samu halartar Mai martaba Sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje CON.
Haka kuma taron ya samu halartar jagororin Fulani da manoma daga sassan daban-daban na karamar hukumar.

Tun da farko an gayyaci malaman addini suka gudanar da jawabai cikin harshen Hausa, Fulatanci da Gizmanci. 

Dayake tsokaci kan jawaban Malam Babban limamin Masarautar Hadejiya Malam Yusuf Abdurrahman Ya'u ya bayyana irin tarin arzikin da Allah ya hore wa yankin wanda shine musabbabin rikicin.

Babban limamin Masarautar Yayi roko ga shugaban karamar hukumar Guri akan a dauki nauyin malaman domin shiga lungu da saƙo na yankin wajen ilmantar da al'umma.

Shima a nasa jawabi Mataimakin Kwamishina 'Yan sanda Adamu Shehu ya bayyana yankin a matsayin yanki mafi hatsari wanda yake barazana ga aikinsu.

Adamu Shehu ya kara da cewa yankin ya zama wata matattarar aikata munanan ayyuka kamar fataucin miyagun kwayoyi.

A karshe ya nemi al'ummar yanki su cigaba da basu haɗin kai domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Da yake jawabi uban ƙasa mai martaba Sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje CON

Ya nuna takaicinsa kan daukan makami da ake a yankin wanda har  yakai ga rasa rai inda ya fada cewa wanda ya dauki makami ya kashe wani makomar sa jahannama ce.
Sarkin Hadejiya Alhaji Adamu Abubakar Maje CON ya kara da cewa wannan arziki da ake rigima kansa Allah ne kan Bama mutum babu yadda za'ayi abinda zaman lafiya bai bada ba rashin sa ya bada.

Haka kuma Sarki ya bada umarnin ga jami'an tsaron kan kama duk wanda yake fatauci da ta'ammuli da miyagun kwayoyi koda ɗansu ne na ciki ko kuma wani mai rike da sarautar.

A karshe Sarkin Hadejia Ya roki al'umma su cigaba da zama lafiya domin bunkasa tattalin arzikin yanki.

Dayake jawabin Godiya Shugaban Karamar Hukumar Guri Alhaji Musa Shu'aibu Guri ya godewa mai martaba Sarkin kan wannan kokari nasa na samar da zaman lafiya a yankin.

Haka kuma ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun sami zaman lafiya da kashi saba'in da biyar cikin ɗari.

Alhaji Musa Shu'aibu Ya kuma gargaɗi masu sare gandun daji Kan su dena ko kuma doka tayi aiki a kansu.

Alhaji Musa Ya roki Mai martaba Sarkin koda shine ya taka doka,doka tayi aiki a kansa.

Ya kuma bayyana ƙudinsa na ginin sabuwar tasha mota, shaguna da nufin  zamanatar da garin dama bunkasa harkokin kasuwanci.

A karshe Alhaji Musa Shu'aibu ya ƙarƙare da ayyukan cigaban da yakawowa yankin kamar ginin Ginin masallatan juma'a a garin Musari wanda lakume zunzurun kudi Naira miliyan goma sha tara, da  Asibiti kwantar da maras lafiya na  miliyan goma sha bakwai a garin Dagana da kuma Samar da ruwan sha mai amfani da hasken rana a mazabar Margado.

Bayan Kammala taron Mai Martaba Sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje CON da tawagarsa sun ziyarci garin Adiyani wanda aka bude sabon masallaci aka gudanar da Sallar Azahar da la'asar.

No comments