Ƴan Takara Shida Sun Janye Daga Takarar Shugabancin APCƳan takara shida masu neman kujerar shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya sun janye kafin babban taron zaɓen shugabanni a Abuja.

Ƴan takarar da suka janye sun haɗa da tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura da George Akume, tsohon gwamnan Benue da tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, da kuma Saliu Mustapha da Muhammed Etsu da kuma Sani Musa.

Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sunayensu da kuma sa hannun tsohon gwamnan Benue ƴan takarar sun ce sun janye wa zaɓin shugaba Muhammadu Buhari tsohon gwamnan Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu.

                  Kwafen takardar

Post a Comment

0 Comments