CIKIN HOTUNA: Sabon Shugaban Jam'iyyar APC Ya Shiga OfisSabon shugaban Jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu daga jihar Nasarawa ya shiga ofis dinsa dake Babbar Hedikwatar Jam'iyyar dake birnin Tarayya Abuja. 

Ya karbi jagorancin Jam'iyyar daga shugaban rikon Jam'iyyar, kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni. 

Taron mika ragamar shugabancin Jam'iyyar zuwa ga sabon shugaban da aka zaba bisa maslaha ya gudana ne a yau Laraba. 

Post a Comment

0 Comments