Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dalilan Da Ya Sa Muka Tsawaita Yajin Aiki –ASUU

  Kungiyar Malaman jami’o’i ta Nijeriya wato ASUU ta tsawaita yajin aikin gargadi da take yi da makwanni takwas. Inda ta bayyana dalilanta...

 


Kungiyar Malaman jami’o’i ta Nijeriya wato ASUU ta tsawaita yajin aikin gargadi da take yi da makwanni takwas. Inda ta bayyana dalilanta na yin hakan.

An dai cimma wannan matsaya ne bayan taron majalisar zartarwa kungiyar malaman jami’o’in na kasa da safiyar ranar Litinin a hedikwatarta da ke Jami’ar birnin Abuja.

Jim kadan bayan taron ne shugaban kungiyar ta ASUU Emmanuel Osodeke ya ce karin wa’adin ya fara aiki ne daga karfe 12:01 na safe na ranar Litinin 14 ga Maris, na shekara ta 2022.

Sanarwar ta bayyana takaicin yadda gwamnati ta ki mayar da hankali wajen kula da bukatun da suka gabatar mata a tsawon tsawon makwanni hudu da suka shafe suna yajin aikin gargadi.

A ranar 14 ga watan Fabarairun da ya gabata ne dai kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya ASUU, ta shiga yajin aikin gargadi na wata daya, domin neman gwamnati ta cika alkawarin mutunta yarjejeniyoyin da suka cimma, wadanda suka ba da damar dakatar da dogon yajin aikin da suka yi a shekarar 2020.


No comments