Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dan Majalisa Babawo Ya Gwangwaje Al'ummar Mazabarsa Da Kayayyakin Dogaro Da Kai

Daga Aisha Suleman Zariya Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Mazabar Sabon Gari Rt. Honorabul Garba Datti Muhammad (Babawo) ya k...


Daga Aisha Suleman Zariya

Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Mazabar Sabon Gari Rt. Honorabul Garba Datti Muhammad (Babawo) ya kaddamar da bayar da kyaututtuka har guda dubu daya da dari daya da talatin da shida (1,136) ga al'ummar Mazabar Sabon Gari a Sakatariyar Karamar Hukumar Sabon Gari dake jihar Kaduna.

Kyaututtukan kuwa sune:-

(1) Kekunan dinki = 256
(2) Injinan nika = 410
(3) Industrial Sewing Machine = 75
(4) Welding machines = 15
(5) Pumping machine = 270
(6) Injinan gyaran waya =10
(7) Kekunan guragu = 55
(8) Keke Napep = 36
(9) Motoci = 9

Wakiliyar mu na daya daga cikin wakilan kafafen labarai da suka shaida yadda taron ya gudana.

A lokacin bayar da kayan Honorabul Datti Babawo ne ya zo da kansa tare da abokan tafiyarsa na siyasa.

A jawabinsa ya yi albishir ga jama'ar karamar hukumar ta sa cewa wannan rabon kayan zai ci gaba da yardar Allah da zarar Allah ya bude hanyar don haka ya yi fatan duk wanda ya samu to ya yi amfani da shi ta hanyar da ya dace.

Alhaji Shehu Namadi Samaru na daya daga cikin wadanda suka sami kyautar Mota a lokacin da yake jawabi ga manema labarai ya nuna farin cikinsa ne tare da godiya ga Dan majalisar kuma ya tabbatar da kara bashi goyon baya a nan gaba da ikon Allah.

Daga cikin manyan bakin da suka marawa Dan majalisan baya yayin rabon akwai babban Darakta a hukumar kula da Addinai na jihar Kaduna Shiekh Abubakar Jamilu Albani Samaru da shugaban karamar hukumar ta Sabon Gari Injiniya Muhammad Usman da babban Sakatare a hukumar bayar da tallafin Ilmi na jihar Kaduna Alhaji Rilwan da dai sauran manyan mutane daga bangarori daban-daban ciki da wajen jihar Kaduna.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.


No comments