Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya EFCC, ta cafke tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano. Wani Ja...
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya EFCC, ta cafke tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.
Wani Jami’in hukumar ya bayyana cewa an kama tsohon gwamnan da ke cikin jerin sunayen mutanen da EFCC ke sa’ido a kan su, a filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas da misalin karfe 8:30 na daren alhamis a lokacin da yake shirin shiga jirgin da zai kaishi birnin Houston na kasar Amurka.
An tsare tsohon gwamnan ne ‘yan lokota bayan da ya mika mulki ga Charles Soludo,tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.
A watan nuwamba na shekarata 2021 ne hukumar EFCC ta mika wasika ga hukumar shige da fice ta kasa na ganin ta sanar da ita a duk lokacin da Willie Obiano ke yunkurin ficewa daga kasar.
No comments