Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AP - Michel Euler Rfi Hausa ta labarto cewa; an kawo karshen saka takunkumi da nuna takardar shaidar k...
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AP - Michel Euler |
Rfi Hausa ta labarto cewa; an
kawo karshen saka takunkumi da nuna takardar shaidar karbar allurar rigakafin
Covid19 a Faransa, matakin da gwamnatin kasar ta dauka a yau Litinin wanda ga
dukkan alamu Faransawa sun yi na’am da shi na kara tabbatar da cewa ana gab da
shawo kan annobar.
Wannan
matakin na nufin cewa Faransawa da ke bukatar zuwa gidajen cin abinci ko kuma
gidan kallo ko kuma shakatawa, hadi da
wuraren baje koli, suna da damar zuwa ba tare da wata tsangawa ba.
Haka
zalika babu batun amsar tambayar rashin dalilin sanya takunkumi, a makarantu,
ko a katafaren kantuna, wanda hakan ke nufin jama’a za su gudanar da harkokin
su ba kamar yadda aka saba ba kafin lokacin dokar kulle.
Amma
gwamnati yanzu haka ta tabbatar da cewa wuraren da ake samun cunkoson jama’a,
misali motocian safa, da asibitoci ya zama wajibi mutane su kare kai, tare da
baiwa kamafanoni masu zaman kan su zabi, ko su ci gaba da amfani da dokar
Covid19 din ko kuma su kyale jama’a haka nan.
An
samu raguwar labarin cuatar Covid-19 akamakon yakin da ake awakana tsakanin
kasashen rasha da kuma Ukraine, a gefe guda kuma batun takarar shugabancin
kasar faransa, inda masana ke ganin cewa annobar da ta kawo tsaiko a bangarori
da daman a duniya ta yi nisa sosai.
A
zahiri, bayan makwanni da samun raguwar yaduwar cutar, hukumomin lafiya a
Faransa sun ce adadin sabbin cututtukan sun haura 73,000 a ranar Juma'a, kadai
daga 60,000 a mako daya da ya wuce.
Abin
da kwararru ke cewa har yanzu shaine, gwamnati kuma ta gaza cimma burinta na
kawo karshen adadin marasa lafiya da ake jibgewa a sashen bada agajin gaggawa
ko kuma killacewa kasa da 1,500.
No comments