Gwamnatin Jihar Naija ta ce ta shiga tsarin Gwamnatin Taraiya mai taken At-Risk Children Project, ARC-P da za a tallafawa sama d...
Gwamnatin Jihar Naija ta ce ta shiga tsarin Gwamnatin Taraiya mai taken At-Risk Children Project, ARC-P da za a tallafawa sama da yara 72,000 da ba sa zuwa makaranta.
Wacce ta shirya shirin kuma mai dakin gwamnan jihar Naija, Dakta Amina Bello ce ta baiyana hakan a Mina, lokacin da ta karbi baƙuncin tawogar ARC-P, bisa jagorancin Maryam Uwais, mai baiwa shugaban kasa shawara a kan shirye-shiryen tallafawa al'umma.
Dakta Bello ta ce gwamnatin jihar za ta yi amfani da shirin domin tallafawa yaran da ba sa zuwa makaranta d akuma magance zaman-banza tsakanin matasa a faɗin jihar da kuma samar musu da sana'o'in da za su riƙe su tsawon rayuwarsu.
Ta danganta matsalolin rashin tsaro da ke gallabar Arewacin Nijeriya da talauci, inda ta ce amfanin shirin ARC-P kenan wajen magance waÉ—annan laifukan.
Ta ce gwamnatin jihar ta dage wajen tallafawa yaran da basa zuwa makaranta domin daga darajar rayuwarsu su zama masu amfani a cikin al'umma.
A nata jawabin, Uwais ta ce an ƙirƙiro da shirin ne domin ya baiwa gwamnati damar tallafawa yaran da basa zuwa makaranta ta hanyoyi daban-daban.
No comments