Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Haihuwar Dabba A Zariya: Ra'ayoyin Likitoci, Malamai Da Masana

             Malam Baiwa Daga Allah Daga Umar Idris Abuja A cikin wannan satin ne wata mata mai suna Murja ta shelantawa duniya ...

             Malam Baiwa Daga Allah

Daga Umar Idris Abuja

A cikin wannan satin ne wata mata mai suna Murja ta shelantawa duniya cewa ta haifi wani abu mai siffar Jaki a wata Anguwa dake kira Tudun Wada a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.

Wannan lamarin ya ja hankalin mutane musamman a Arewacin Nijeriya saboda wani lamari ne bako a zamantakewar Dan Adam kuma a al'adance.

Bisa haka ne manema labarai suka dukufa don jin ra'ayin masana akan lamarin. Shahararren Jami'in tsaron nan mai aiki karkashin rundunar hukumar 'yan Sanda na kasa dake jihar Kaduna kuma mai bayar da maganin cututtuka cikin gida da waje shima ya tofa albarkacin bakinsa akan wannan lamarin.

Malam Baiwa daga Allah ya bayyana nasa ra'ayin game da wannan abu mai cike da ban mamaki da al'ajabi. 

Amma da farko ya fara ne na yin godiya ga Allah madaukakin Sarki tare da yin salati ga Annabin Rahama Muhammad (SAW).

Bayan haka sai ya ce, shi a ganinsa wannan lamari babu wani abin mamaki a cikin lamarin saboda babu abin da yafi karfin Allah. Malamin ya kara da cewa   Allah zai iya yin abin da yafi haka don ya nuna girmansa ga bayinsa. 

Don haka Malamin ya ce irin wannan abu yana faruwa musamman idan Allah ya so ya gwada ikonsa. Ya ce shi kanshi ya kan gamu da ire-iren wannan cututtuka ga mutanen da yake bai wa taimakon magani. Karshe ya ja hankalin mutane da cewa karyata ire-iren wannan lamarin kuskure ne saboda Allah na iya yin komi bisa ikonsa.

Sheikh Aliyu Abdullahi Teleks Babban Malami ne kuma Babban Limami ne a Masallacin Tudun Jukun Zariya kuma shugaban majalisar Malamai ta JIBWIS jihar Kaduna a yayin da yake yi wa manema labarai jawabi akan lamarin haihuwar Dabba da Malama Murja ta yi a Tudun Wada Zariya ya ce; "Gaskiya akwai shakku mai yawa a cikin wannan lamarin bisa ga koyarwar addinin Islama domin wani jinsi ba ya haihuwar wani jinsi duk da cewa akwai masu yin sihiri amma ko da hakan bai zama wannan lamarin ya zama gaskiya ba.

                   Sheikh Aliyu Teleks

Don hakan ne Shehin Malamin ya ja hankalin jama'a akan irin wannan sihirin kuma ya bayar da misali da wani mutum da ya ce zai fitar da wani maciji a wata Daga da ake yawan hadari a Zariya daga karshe lamarin ya tabbata ba gaskiya bane illla surkulle don haka ya ce, wannan ma nan gaba jama'a za su gane gaskiyar lamarin tunda ance ba haihuwar ta ta yi ba kamar yadda ake haihuwar da ta al'aura wannan mai bayar da maganin shafa cikin tayi kawai sai ga Dabba a matsayin shi ne abin dake cikin don haka ne Malamin ya yi kira da a guji yin imani abubuwan da ka iya zama shirka.

Haka zalika manema labarai sun nemi jin ta bakin likitocin kimiyyar Dan Adam na Asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello Zariya wato ABUTH. 

Dakta Hasan Abubakar shi ne shugaban Likitoci reshen Asibitin Tudun Wada Zariya (Medical Center) dake karkashin Asibitin koyarwa na Jami'ar ta Ahmadu Bello Zariya.

      Dakta Hassan Abubakar Mukhtar

Shima cewa ya yi; "maganar Bil Adama ya haifi wani jinsi da ba Mutum ba a ilimin zamani (Boko) hakan ya saba wa hankali amma akan sami mutum ya haifi mutum babu kafa ko wani sashi na jiki.

Don haka maganar cewa wata ta haifi Akuya ko Jaki a gaskiya wannan lamari akwai ayar tambaya akan lamarin.

Dakta Hassan Abubakar ya bayar da misali da cewa wata rana wani mutum mai dauke da ciwon kaba ya sanar damu cewa cutar (kabar) na damunsa amma wani ya bashi magani ya shafa a wajen (kabar) sai Kadangare ya fito da nufin an cire masa (kabar) kuma hakan ba gaskiya bane illa sihiri da wasu suke yi wajalen bayar da maganin gargajiya.

Karshe Likitan ya sanya ayar tambaya akan haihuwar wannan dabba da Malama Murja ta ce ta haihu ta hanyar taimakawar wata mata mai bayar da magani. 

Shi ko Dakta Ubale mai maciji Samaru masani kan al'amuran gargajiya a kasa baki daya cewa yayi; "Tabbas Aljani kan shiga cikin jikin Bil Adama har ya haddasa masa ciwo mai tsanani don haka samun mutum ya haifi dabba ba abin mamaki bane don haka haihuwar da Malam Murja ta yi shi bai bani wani mamaki ba amma da a yi kokarin kaucewa shirka da surkullen wasu mutane da suke so su yi kudi kota wani hali.

                       Dakta Ubale 

Ya zuwa hada wannan rahoto mutane ne suke dandazo zuwa gidansu Malama Murja don ganewa idonsu abin mamaki.

Amma bincike ya nuna cewa shi Dabbar da Murja ta ce ta haifa  ba haihuwarsa ta yi ba kamar yadda ake haihuwar kowa ta (Farji) amma Murja ta tabbatar da cewa mai bayar da maganin shafata ta yi akwai sai ga Dabban ta fado.

Haka zalika Malama murja ta bayyana cewa ta kan je asibitin Dakta Umar don yin awon ciki amma ba a ganin komi illa ruwa tsundum amma yau ga shi Allah ya nuna mata ikonsa ta ga abin dake cikinta.

        Malama Murja wacce ta haifi 'Jaki'.

Bincike ya tabbatar da cewa kaso da yawa na kawo shakku akan lamarin bisa yadda lamarin ya zama abin almara.

                Jakin da aka haifa. 

No comments