Daga Ammar M. Rajab Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana takaicinsa game da yadda ayyukan ta’addanci ke yawaita mu...
Daga Ammar M. Rajab
Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana takaicinsa game da yadda ayyukan ta’addanci ke yawaita musamman a Arewacin Nijeriya. Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayani dangane da halin da ake ciki, musamman kan abin da ake kira ‘Bandits’ ko Mahara a yanzu.
Shaikh Zakzaky ya bayyana takaicinsa kan yadda ake ta kashe a’umma da sunan mahara ba tare da wani bayyanannen dalilin akan yin hakan ba. Malamin ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da wakilai daga al’ummar Fulani mai suna ‘Kautal Ko’e Julbe’ suka kai mishi a gidanshi dake Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.
“Sai a ka ce mahari, hari kawai ya ke yi, babu wani dalili, sai ya kai hari, kuma ba ya sata, in ya shiga gari sai ya harbe mutane ya cinna wa gidajensu wuta, sai kuma ya kona rumbun abinci, inda suka tara hatsinsu na shekara, ya kokkona, ko kuma ya yamutsa dawa da gero da wake, ya yamutsa ya watsar. Kuma bashi da dalili illa (kawai shi Mahari ne) ya na kai hari ne.” Inji Zakzaky
Malamin ya kara da cewa; abin da suke so shi ne za su share mutanen da ke wannan yanki na Zamfara su yi filayen jiragen sama su dibi zinare. Haka abin da suke yi ke nan tsakanin Zariya da Birnin Gwari.
Har ila yau ya ba da labarin irin salon da aka rika bi da matakai daban-daban wajen kulla wannan makircin har aka kawo inda ake yanzu. “Bayan suna hare-hare irin wannan, sai suka bullo da Banga. ‘Yan banga din musamman ya zama sai suka fara farwa Fulani, Fulani suke kai wa hari musamman.”
Malamin ya karkare maganarshi da cewa; ya zama lokacin da muke tsare abin ya yi kamari, shekarar da aka tsaremu sai kawai aka tura sojoji zuwa yankin Zamfara, suka je suka dinga harbe Fulani, wai barayin shanu ne, sai ana kada shanun na su, wai barayin shanu, kuma soja ke yi.
Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Yanzu bamu da wani mafita illa mu koma ga Allah, mu yi ta addu’a, Allah Ta’ala ne kawai zai kwace mu.
No comments