Fashewar ta faru ne a lokacin da masu ibada suka taru a masallacin Kucha Risaldar da ke tsohon birnin Peshawar domin yin sallar Juma'...
Fashewar ta faru
ne a lokacin da masu ibada suka taru a masallacin Kucha Risaldar da ke tsohon
birnin Peshawar domin yin sallar Juma'a.
Wani bam mai
karfi ya fashe a cikin wani masallacin 'yan Shi'a da ke birnin Peshawar a arewa
maso yammacin Pakistan a ranar Juma'a, inda ya kashe mutum fiye da 30 tare da
jikkata wasu da dama, da dama daga cikinsu sun samu mummunan rauni.
Fashewar ta faru
ne a lokacin da masu ibada suka taru a masallacin Kucha Risaldar da ke tsohon
birnin Peshawar domin yin sallar Juma'a, in ji 'yan sanda.
Motocin daukar
marasa lafiya sun bi ta cikin titunan mai cike da mutane dauke da wadanda suka
jikkata zuwa asibitin Lady Reading. Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
An kai hare-hare
makamantan wannan a yankin da ke kusa da kan iyaka da kasar Afganistan.
Shayan Haider, ganau
ne, yana shirin shiga masallacin, lokacin da fashewar mai karfi ta jefa shi kan
titi.
"da na bude
idona, sai na kura da gawarwaki a ko'ina," in ji shi.
A sashen bayar
da agajin gaggawa na asibitin Lady Reading, an shiga rudani a yayin da likitoci
ke fafutukar matsar da wadanda suka samu raunuka zuwa wuraren tiyata.
Firaminista
Imran Khan ya yi Allah wadai da tashin bam din.
No comments