Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa kan harin da ‘yan ta’adda suka kai kan jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a ranar Liti...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa kan harin da ‘yan ta’adda suka kai kan jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a ranar Litinin da ta gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Shugaban
kasar a ranar Talata ya ce ya damu matuka da harin, wanda shi ne irinsa na biyu
a ‘yan kwanakin nan.
Buhari
ya yi Allah-wadai da harin bam da aka kai kan jirgin fasinjan, yana mai bayyana
hakan a matsayin “al’amari mai matukar kaduwa.”
“Harin
da aka kai kan jirgin kasan, abin takaici ne; kuma muna jajantawa iyalan
wadanda suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka,” in ji shugaban a wata
sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman, Malam Garba Shehu ya fitar.
Buhari
ya ba da umarnin a gaggauta kammala dukkan matakai na aiwatar da tsaro kan
hanyoyin jiragen kasa na Abuja zuwa Kaduna da Legas zuwa Ibadan.
Ya
kuma umurci hukumar kula da layin dogo ta Nijeriya da su gaggauta gyara layukan
da suka lalace tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba
tare da bata lokaci ba.
“Shugaban
ya bayar da wadannan umarnin ne a Abuja, Talata, bayan ganawarsa da hafsoshin
tsaro karkashin jagorancin babban hafsan tsaro na kasa, Janar Lucky Irabor; da
babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya; da shugaban hafsan sojin sama, Air. Marshal
Isiaka Amao; da Sufeto Janar na ‘yan
sanda, Usman Baba; da Manjo Janar Samuel Adebayo, shugaban hukumar leken asiri
na tsaro; da kuma babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, Yusuf
Magaji Bichi a fadar gwamnati,” inji sanarwar.
No comments