Sakamakon kazamin harin da ‘Yan bindiga a Nijeriya suka kai akan jirgin fasinjar dake zirga zirga tsakanin Kaduna zuwa Abuja wanda yayi sa...
Sakamakon
kazamin harin da ‘Yan bindiga a Nijeriya suka kai akan jirgin fasinjar dake
zirga zirga tsakanin Kaduna zuwa Abuja wanda yayi sanadiyar kashe mutane 7 da
kuma jikkata wasu da dama, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira taron
shugabannin hafsoshin tsaro na gaggawa domin tattauna matsalar.
Rahotanni
sun ce shugaban ya bayyana bacin ransa da lamarin wanda ya kaiga rasa rayuka,
inda ya bukaci hafsoshin tsaron da su kara kaimi wajen murkushe ‘Yan bindigar
dake zafafa hare haren su a wannan lokaci.
Buhari wanda ya bukaci kubutar da
duk fasinjojin da aka sace da kuma tabbatar da ganin an hukunta wadanda suka
aikata laifin, ya kuma baiwa hafsoshin tsaron umurnin harbe duk wanda aka gani
yana dauke da bindiga kirar AK47 ba tare da izini ba.
Shugaban
kasar yace ba zasu lamunce yadda wasu ke hana jama’a zaman lafiya ba, kuma
kamar kowanne dan Najeriya shima ya kadu da wannan hari wanda shine irin sa na
biyu wanda ya kaiga rasa rayuka da kuma jin rauni.
Kafin dai gudanar da taron,
shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahya ya garzaya Jihar Kaduna
inda aka samu hadarin domin ganewa idan sa halin da ake ciki, inda ya umurci
dakarun sa da su gaggauta kubutar da wadanda ‘Yan bindigar suka sace.
Wata fasinjar jirgin da ta
tsallake rijiya da baya, ta bayyanawa RFI Hausa cewar zuwan jami’an soji da
‘yan sanda ne ya kubutar da su daga hannun ‘Yan bindigar wadanda suka fara
kwashe mutane suna kaiwa daji.
Wani
fasinja kuwa ya tabbatar da mutuwar mutane 7 sakamakon harin, yayin da wasu da
dama suka samu raunuka, cikin su harda tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara
Ibrahim Wakalla Mohammed.
Tuni
mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ziyarci birnin Kaduna domin
ganewa idan sa halin da ake ciki da kuma ziyarar fasinjojin da suka samu raunuka
sakamakon kazamin harin.
Wannan hari na zuwa ne kwana biyu
bayan wanda ‘Yan bindigar suka kai kusa da tashar jiragen saman Kaduna, abinda
ya kaiga hallaka 12 daga cikin su.
No comments