Alhaji Ismail Kargi, tsohon shugaban ƙungiyar masu noman albasa ta kasa reshen jihar Kaduna. Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar...
Alhaji Ismail Kargi, tsohon shugaban ƙungiyar masu noman albasa ta kasa reshen jihar Kaduna.
Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar masu noma da sarrafa albasa ta ƙasa ta shelanta dakatar da shugabanta na jihar Kaduna, Alhaji Ismail Kargi daga mukaminsa a fadin jihar baki daya.
Wannan sanarwan ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar na ƙasa baki daya, Alhaji Aliyu Binji. Da shugaban yake bayani akan muhimman dalilan da yasa suka wartaki shugaban na jihar na Kaduna; ya ce a kwanakin baya wasu daga cikin 'ya'yan ƙungiyar sun kawo wa Uwar ƙungiyar koke akan dakatar da shugaban mata na ƙungiyar ta jihar Kaduna Hajiya Hauwa'u Ibrahim Zariya da Alhaji Isma'il Kargi ya yi bisa wasu dalilai nasa na kashin kansa.
Hakan yasa Uwar ƙungiyar na ƙasa ta dauki matakin kiran bangarori biyun don jin ta bakinsu don yin sasanci a tsakaninsu karkashin jagorancin shugaban na ƙasa.
Wannan taron sasanci ya gudana ne a jihar Kaduna a madadin ƙungiyar ta ƙasa baki daya.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa ya ce yayin gudanar da taron ne Sakataren ƙungiyar na jihar Kaduna ya nuna dabi'a ta rashin biyayya ga ƙungiyar daga bisani ya fice daga wajen taron ba tare da izinin shugaban taro ba wanda hakan ya sabawa dokokin ƙungiyar kuma ya ci mutuncin shugaban ƙungiyar da yazo don yin sasanci ga juna.
Hakazalika shima shugaban ƙungiyar ta jihar Kaduna Alhaji Isma'ila Kargi shima nan take ya take dokokin ƙungiyar shima ya umurci da yawa daga cikin membobin ƙungiyar da su tashi su fice daga wajen taron ba tare da izinin shugaban taro ba.
Bisa haka ne Uwar ƙungiyar ta ƙasa baki daya ta zauna tare da daukan matakin tsige shugaban na jihar ba tare da wani ba ta lokaci ba.
Bayan haka Uwar kungiyar ta sanar da cewa daga 25/3/2022 ta dakatar da Alhaji Isma'il Kargi a matsayin shugaban ƙungiyar masu noma da sarrafa albasa na jihar Kaduna baki daya.
Haka zalika Uwar ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin gwamnati da dukkan ƙungiyoyi da Cibiyoyi na ƙasa baki daya da kar su kara yin wata mu'amula da shi a matsayin shugaban ƙungiyar masu noman albasa da sarrafa ta na ƙasa baki daya har illa masha Allah.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Alhaji Ismail' Kargi ta wayarsa ta salula amma lamarin ya gagara. Hakazalika shima shugaban ƙungiyar ta ƙasa shima mun nemi jin ta bakinsa bayan bayanin da ya fitar amma shima ba mu same shi ba.
Ya zuwa hada wannan labarin akasarin 'ya'yan ƙungiyar ta masu noma da sarrafa albasar a kananan hukumomi sai murna suke yi.
Ku biyo mu don jin dalilansu na yin murnar tsige shugaban na su na jihar Kaduna a wannan lokacin.
No comments