Jirgin Yakin Soji Ya Kashe 'Yan Bindiga Sama Da 20 A Neja

 


Majiyoyi sun ce  jirgin ya hango ‘yan bindigar  da dama ne bisa babura, inda ake zaton cewa suna shirin kaddamar da hare hare ne nan gaba kadan.

Luguden wutan ya lalata babura sama da 20 da dimbim ‘yan bindiga, lamarin da ya dadada ran al’ummomin da ke yankunan na mariga da ke fama da ta’addancin ‘yan bindiga.

‘Yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’addan ISWAP ne sun mamaye wasu yankunan jihar Neja, inda suke cin karensu babu babbaka.


Post a Comment

0 Comments