Wata babbar kotun Tarayya dake jihar Kano, ta bada umarnin a ɗebo kudi a dukkan asusun ajiya na mai magana da yawun rundunar ...
Wata babbar kotun Tarayya dake jihar Kano, ta bada umarnin a ɗebo kudi a dukkan asusun ajiya na mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a biya wani matashi mai suna, Bashir Galadanci, kudin diyyar da kotun ta ce a bashi, kusan shekara guda ke nan da ta gabata.
Nasara Radio 98.5 FM ta labarto cewa; Lauyan mai kara, Barista Abba Hikima, ya ce tun farko an bukaci Kiyawa ya biya matashin kudi naira Miliyan guda, sannan ya shiga kafafen watsa labarai ya bashi hakuri, amma bai yi ko guda ba, shiyasa kotun ta ce a ɗebo a asusunsa, wanda yanzu an samu Naira dubu dari uku, kuma za a ci gaba da neman ragowar, a cewar Hikima.
No comments