Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kungiyar Manyan Ma’aikata, SSANU Na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Ta Yi Sabon Shugaba

Sabon shugaban kungiyar SSANU reshen ABU Zariya, Malam Muhammad A. Yunusa . Daga Aisha Suleman, Zariya A cikin satin da ya gabata ne...

Sabon shugaban kungiyar SSANU reshen ABU Zariya, Malam Muhammad A. Yunusa.Daga Aisha Suleman, Zariya

A cikin satin da ya gabata ne kungiyar manyan ma’aikatan Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (SSANU) ta sami nasarar gudanar da zabe don samun tabbataccen shugaba a kungiyar da sauran kujeru masu muhimmanci da aka kwashe shekaru masu yawa babu kowa a kansu sakamakom rigingimu da rikita-rikita da kungiya ta fada .

Bisa yardar Ubangiji sai ga shi a wannan karo an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba. Wakilanmu na daya daga cikin wakilan kafafen watsa labarai da suka shaida yadda zaben ya gudana a wannan rana.
Shi zaben an gudanar da shi ne a wurare daban-daban ne kamar ma’aikatan shiyyar Kongo da I.A.R da sauran tsangayoyi da suke karkashin kungiyar ta SSANU duk sun gudanar da zabensu ne a inda suke daga bisani ne aka tattara kuri’un zuwa babban wurin taro na Mamman Kontagora dake harabar Jami’ar don kirga su.

Bayan da hukumar zaben suka gama kirga dukkan kuri'un kowanne dan takarar ne bisa kulawar dukkan wakilan 'yan takarar sai aka ajiye kuri’un zuwa wayewar gari.

A washe gari ne hukumar zaben ta kira yi dukkan wakilan 'yan takara zuwa hawa na 3 a babban bene na hukumar Jami’ar wato (hawa tara) don tantance kuri’ar da kowanne dan takarar ya samu kuma haka ya gudana bayan an tabbatar da duk wani nan takarar ga abin da ya samu sai aka dunguma zuwa babban dakin taro na Assembly Hall don shelanta wanda suka sami nasara.

Bayan gabatar da dukkan wanda suka sami nasara ne a kujeru kusan guda 8 sai aka bayyana Malam Muhammad A. Yunusa a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kungiyar da kuri’u 839 inda abokin takararsa Malam Shuaibu Kakil ya sami 448 sai Mista Galmaka ya sami kuri’u 411 wanda hakan yasa Muhammad A.Yunusa ya sami damar zama shugaban kungiyar ta SSANU reshen Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.

Bayan an rantsar da dukkan wanda suka sami nasara ne wakilanmu sun sami zantawa da shi wanda ya jagoranci gudanar da tsara dukkan harkar zaben, Malam Bashir inda ya nuna jindadinsa da aka ba shi damar tsara zaben ga shi cikin ikon Allah an yi zaben lafiya an gama lafiya. Karshe ya yi kira ga sabon shugaban kungiyar da ya ji tsoran Allah yayin da yake gudanar da shugabancinsa ya ce, yakamata ya rungumi kowa a kungiyar don kawo ci gaba a kungiyar baki daya. 

Shi ko zababben shugaban yayin da ya gama rattaba hannu a takardar rantsuwar ya yi wa 'ya'yan kungiyar albishir na tafiyar da kungiyar zuwa ga nasara kuma ya yi godiya ga dukkan 'ya'yan kungiyar da suka ba shi goyan baya da har ya kai shi ga samun nasara .

Haka zalika yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ya gama cika duk wani sharadin zama cikakken shugaba tare da sauran wadanda suka sami damar darewa kan sabbin kujerun; sabon shugaban ya yi godiya ga shuwagabanin kungiyar ta SSANU kasa da shiyya da duk wadanda suka sa hannu a wajen gudanar da zaben ya gudana cikin tsari. 

Sabon shugaban ya yi alkawarin zai tafi da kowa ya ce, kofa a bude take ga dukkan wanda zai kawo shawara ko gyara don samun ci gaban kungiyar. 

Daga cikin manyan bakin da suka zo wajen wannan bikin rantsuwar akwai tsohon shugaban kungiyar Alhaji A Bello da tsohon mataimakin kungiyar Malam Shuaibu Khalil da mataimakin shugaban kungiyar ta kasa a shiyyar Arewa maso gabas, Alhaji Abdulmalik da dai sauran manyan baki da suka wakilci kungiyar daga Tarayya baki daya.

An yi taro lafiya an tashi lafiya. 

No comments