Matan da suka taru ƙarƙashin ƙungiyoyi daban-daban, sun ce zaman dirshan za su yi a bakin ƙofar. "Ba za mu bar wajen nan ba har sai m...
Matan da suka taru ƙarƙashin ƙungiyoyi daban-daban, sun ce zaman dirshan za su yi a bakin ƙofar.
"Ba za mu bar wajen nan ba har sai mun ga shugaban majalisa, sai majalisa ta bai wa mata 'yancinsu," a cewar Niri Goyit daga ƙungiyar Action Aid.
Lamarin ya faru duk da cewa Matar Shugaban Ƙasa Aisha Buhari ta je majalisar da kanta a makon da ya gabata don gane wa idonta da kuma tabbatar da cewa ƙudirorin mata sun samu karɓuwa a gyaran kundin tsarin mulkin.
A yau Laraba ne 'yan majalisar za su kammala kaɗa ƙuri'a kan batutuwa kusan 60 da suka shafi gyaran ɓangarori daban-daban na kundin mulkin.
No comments