Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya kawo karshen zamansa a cikin Jam’iyyar PDP mai alamar lema, inda ya sanar da ficewarsa ...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya kawo karshen zamansa a cikin Jam’iyyar PDP mai alamar lema, inda ya sanar da ficewarsa daga cikin jam’iyyar.
Kwankwaso ya rubuta wa shugaban mazabarsa inda ya
bayyana godiya akan mu’amala mai kyau da suka yi a shekarun da ya kwashe suna
aiki tare a matakin mazaba, karamar hukuma, jiha da kuma kasa baki daya.
Tsohon gwamnan ya ce sakamakon wasu dalilai na
rashin fahimtar juna, ya yanke hukuncin ficewa daga jam’iyyar daga ranar
Talata, 29 ga watan Maris na shekarar 2022.
Kafin dai wannan lokaci an dade ana rade radin cewar
Kwankwaso zai sauya sheka zuwa Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari domin
tsayawa takarar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Tuni wasu daga cikin magoya bayansa suka fice daga
PDP domin komawa sabuwar Jam’iyyar a jihar Kano da kuma wasu jihohi dake cikin
kasar.
No comments