Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

La Liga: Barcelona Ta Yi Fata-fata Da Real Madrid

A fatawar gasar Laliga, mako na 29,  tsakanin Real Madrid da Barcelona, Barca ta bi Madrid har gida ta lallasa ta da 4-0 a wasa ...A fatawar gasar Laliga, mako na 29,  tsakanin Real Madrid da Barcelona, Barca ta bi Madrid har gida ta lallasa ta da 4-0 a wasa mai taken El Clasico.

Pierre Emerick Aubameyang ne ya fara jefa kwallo a ragar Madrid tun a minti na 29. 

Kamar wasa, ashe cin da Aubameyang ya yi, ya karya asirin ragar Madrid me, inda a minti na 38, R. Araujo ya ƙara.

A minti na 47, jim kaɗan bayan dawo wa da ga hutun rabin lokaci, ai kuwa sai kwallon ta uku ta faɗa ragar Madrid ta hannun yaron nan mai tashe, Ferran Torres, inda daga bisani Aubameyang ya ƙara ƙwallo ta huɗu a minti na 51.

Wannan wata gagarumar nasara ce ga Barcelona, musamman ganin cewa ƙungiyar ta fara kakar bana da rashin kokari.

Sai dai kuma tuni Barcelona su ka fara farfaɗo wa a hannun sabon koci kuma tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Xavi Hernandez.

Da yawa sun zaci Madrid za ta doke Barcelona ganin yadda Madrid ɗin ke tashe, sai gashi Barca ta zamto ɗan hakin da ka raina.

No comments