Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Labari Mai Sosa Zuciya Na Wani Fasinja Da Ya Mutu A Harin Jirgin Ƙasan Abuja Zuwa Kaduna

Hausa Daily Times ta labarto cewa; wani wanda harin jirgin ƙasan Kaduna ya rutsa da bai jikkata ba, ya ce, "Ina zaune a cik...


Hausa Daily Times ta labarto cewa; wani wanda harin jirgin ƙasan Kaduna ya rutsa da bai jikkata ba, ya ce, "Ina zaune a cikin jirgi ina karatun Qur'ani, sai aka bugo ma wani mutun waya. Mutumi sai ya yi sauri ya ɗauki wayar kalmar farko da ta fito daga bakin sa ita ce 'Noor', a ƙarshe dai na ce wannan daga ji matarsa ce. "Ba zan iya jin abin da suke faɗa ba, kan ka ce kwabo ji kawai muka yi wani abin fashewa mai mugun ƙara ya tashi wanda ya tilasta katse wayar da mutumin ke yi, sai harsasai suka fara kutsowa cikin jirgin babu kakkautawa, mintuna kaɗan da lafawan harbin, sai muka duba juna, abin da na gani ya yi muni, mutumin da ke waya ganin shi na yi kwance a ƙasa ya mutu kuma ga wayarsa a ƙasa magana na ci gaba da fitowa, na ɗauki wayar, abu na gaba da na ji shi ne 'Baby na ji ƙara mara daɗi, fatan lafiya', na kasa ba da labarin halin da mijinta yake ciki, na kasa ce mata ya rasu, na firgita sossai ina ta kuka. Bayan minti ɗaya sai ta aika da sakon cewa "na dafa maka abincin da ka fi so", lokacin da jami'an tsaro suka iso na miƙa musu wayar na ce musu wayar wannan mutumin da ke kwance ne, na yi kuka na fitan hankali, na kasa barci a wannan rana." .

No comments