Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Lai Ya Bai Wa Gwamnati Kariya, Ya Ce Tsadar Abinci Da Mai Duk Duniya Ne

Gwamnatin Tarayya ta ce tashin farashin  kayan abinci, man fetur, dizalel da sauran kayayyaki ya zama ruwan dare gama duniya, ba...


Gwamnatin Tarayya ta ce tashin farashin  kayan abinci, man fetur, dizalel da sauran kayayyaki ya zama ruwan dare gama duniya, ba wai kawai wata Æ™asa guda É—aya ba.

Ministan YaÉ—a Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a yau Litinin a Abuja, ya kara da cewa taÆ™aita matsalar ga Najeriya kaÉ—ai to ya zama yarfe da tsabagen yaÉ—a kalaman Æ™arya.

Ya ce ƙididdiga da ƴan adawa da wani ɓangare na kafafen yaɗa labarai da su ke kwatanta farashin wasu kayan abinci, man fetur, dizel, kafin shekarar 2015 da kuma a halin yanzu, yarfe ne kawai.

“Wannan lissafin domin rano da kididdiga ba gaskiya bane. WaÉ—anda su ke amfani da waÉ—annan Æ™ididdiga ba tare da sanya su cikin mahallin ba to ba su san ma mai sunkenyi ba .

“Mu dauki farashin kayan abinci da man fetur. A duba shafin Google a ga farashin kayan abinci a wasu Æ™asashe, musamman Burtaniya da Amurka, za ku ga cewa yayi tashin gwauron zabi. Ba ma a managar farashin iskar gas ko man fetur, '' in ji shi.

Ministan ya kara da cewa matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a fadin kasar nan a ‘yan kwanakin nan ya fara samun sauki, yayin da matakan da gwamnati ta dauka sun fara aiki.

Ministan ya ce matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a fadin kasar nan a Æ´an kwanakin nan ya fara samun sauki, yayin da matakan da gwamnati ta dauka sun fara aiki.

No comments