Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Magoya Bayan PSG Sun Yi Wa Messi Da Neymar Ihu

  Magoya bayan Paris Saint-Germain a gasar Ligue 1 ta kasar Faransa, sun yi wa fitattun ‘yan wasan kungiyar da suka hada da Lionel Messi da ...

 


Magoya bayan Paris Saint-Germain a gasar Ligue 1 ta kasar Faransa, sun yi wa fitattun ‘yan wasan kungiyar da suka hada da Lionel Messi da Neymar ihu a ranar Lahadi, yayin buga wasansu na farko tun bayan da Real Madrid ta fitar dasu daga gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba.

PSG da ke jagorantar gasar ta Ligue 1 sun fafata ne da Bordeaux, inda kuma magoya bayan ta suka rika yi wa 'yan wasan kungiyar ihun adawa da kuma fito a duk lokacin da suka taba kwallo, musamman ma Messi da Neymar.

Sai dai Kylian Mbappe, wanda mai yiwuwa ya koma Real Madrid nan gaba kadan, bai fuskanci bacin ran masu kallon ba, kasancewar ya taka rawar gani wajen cin kwallaye a dukkanin karawar da suka yi da jagororin na gasar La Liga ta Spain.

Daga karshe dai kungiyar PSG ta samu nasara kan Bordeaux da kwallaye 3-0, wadanda Mbappe da Neymar da Paredes suka jefa.

A halin yanzu kungiyar ke kan gaba a gasar Ligue 1 da maki 65, tazarar maki 15 a tsakaninta da Marseille, waddake matsayi na 2.


No comments