Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Majalisar Kitabu Wassunnah Ta Ƙaddamar Da Littafi A Zariya

    Sheikh Muhammad Nazifi Hashim, Shugaban majalisar Kitabu Wassunnah Samaru Zariya.   Daga Aisha Suleman Kaduna Majalisar Kita...

    Sheikh Muhammad Nazifi Hashim, Shugaban majalisar Kitabu Wassunnah Samaru Zariya. 

Daga Aisha Suleman Kaduna

Majalisar Kitabu Wassunnah ta kaddamar da littafi mai suna 'Bayanul Hakikatus-Sunnatil Nabawiyyah' wanda Sheikh Muhammad Nazifi Hashim Samaru ya wallafa.

Wakilamu sun sami halartar wannan taro. Taron an gudanar da shi ne a babban dakin taro dake Cibiyar Nazarin Aikin Gona na Jami'ar Ahmadu Bello Zariya (IAR).

Wannan littafi dai majalisar Kitabu Wassunnah ce ta wallafa shi karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Nazifi dake lamba 17 kan titin Sarkin Huda a hayin Dogo Samaru Zariya karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Kuma an kaddamar da littafin ne don taimakawa shirin gina makarantar marayu da majalisar ke kokarin tabbatarwa karkashin kungiyar Izalatul Bidi'a wa'ikamatussuna ta kasa.

Cikin ikon Allah taron ya sami karbuwa ta bangaren manyan malamai da manyan 'yan siyasa da masu kudi har da 'yan kasuwa na cikin jihar ta Kaduna da wajenta baki daya.

Bayan halartar manyan baki ne aka bayar da dama ga Malamai don gudanar da wa'azin da zai karfafa wa jama'a wajen taimakawa addini a wannan lokacin.

Sheikh Teleks Kaduna da Sheikh Jamilu Abubakar Albani Samaru na daga cikin Malaman da suka gudanar da jawabai a wajen wannan taro.

Bayan manyan Malamai da sauran manyan baki sun gudanar da jawabi ne sai shugaban kwamitin taro ya bayar da damar kaddamar da shi littafin a nan take. 

Bayan jama'a da dama sun fanshi littafin tare da bayar da gudummawa mai tsoka ne, shugaban karamar hukumar Sabon Gari Injiniya Muhammad Usman ya yi jawabi dake nuna godiya ga dukkan wadanda suka zo don taimakawa masu niyyar assasa cibiyar taimakawa marayun a karamar hukumarsa kuma shima ya bayar da gudummawa mai tsoka tare da yin fatan alheri ga daukacin jama'ar da suka  sami damar halartar taron.

Shima shugaban majalisar Sheikh Muhammed Nazifi Hashim a nasa jawabin ya kawo muhimman dalilai da yasa suka dage don taimakawa marayun musamman a irin wannan lokacin da ake fama da matsalar tsaro.

Ya ce sun dade suna gudanar da harkar taimakawa marayu ta hanyoyi daban-daban.

Karshe ya yi kira ga masu hannu da shuni da cewa hanya a bude take ga duk mai niyyar bayar da nashi gudummawar kuma ya yi fatan duk wanda yazo taron Allah ya mayar da shi gida lafiya.

Daga cikin manyan bakin da suka sami damar zuwa wajen taron akwai Honorabul Isa Hazo da babban Darakta a hukumar kula da addini na jihar Kaduna Shiekh Albani Samaru da shugaban karamar hukumar Sabon Gari Injiniya Muhammad Usman da Honorabul Sadiq Ango Abdullahi da sauran manyan mutane daga bangarori daban-daban.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments