Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Makarantar Markazut’ta’alimil Islamiyya Ta Yi Sauka Da Haddar Alkur'ani Karo Na Biyu

Daga Idris Umar, Zariya  A cikin satin da ya gabata ne makarantar Markazut’ta’alimil Islamiy ta yi bikin sauka da haddar Alkur’a...



Daga Idris Umar, Zariya 

A cikin satin da ya gabata ne makarantar Markazut’ta’alimil Islamiy ta yi bikin sauka da haddar Alkur’ani mai girma karo na biyu.

Wakilinmu ya sami halartar wannan taro kuma ya aikowa masu karatunmu da tsarabar abin da ya wakana a wajen taron kamar haka; 

Taron an gudanar da shi ne a babban filin dake mallakin makarantar a garin Falladan karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Bayan manyan baki da iyayen dalibai da aminan arziki sun gama isowa ne sai shugaban taro ya bayar da izinin bude taro da addu’u’a kamar yadda aka saba.

Bayan an bude taro da addu’ar sai shugaban makarantar Malam Abdullahi Jibril Falladan ya zo ya bayar da tarihin makaranta inda ya ce ita dai wannan makarantar sun kafata ne a ranar 1 ga watan Janairun 2011 da ajin karatu guda biyu, ya ce cikin ikon Allah kafin sukai sauka ta farko Allah yasa sun mallaki fili da aji duda 10.

Shugaban ya ce sun yi sauka na farko ne a shekarar 2018 ya ce, cikin nasara bayan saukan ne suka sayi fili guda 2 kuma sun sami damar katange filin tare da gudanar da wasu muhimman aiki kamar yin filasta da yin silin don bunkasa harkar karatun da karfafa daliban makaratar da iyayen yara. 

Shugaban ya ce a yayin da dalibai suka yi masu yawa ne sai suka karbi gidan dake makwabtaka da makarantar sai suka gina mai shi mai gidan dakuna shida a wani  sashi, hakan yasa makarantan ta sami karin azuzuwa masu yawa.

Shugaban ya mika godiyarsa ga Honorabul Bashir Sakadadi bisa wani namijin kokari da ya yi na gina wani aji da ya yi a cikin makarantar.

Shugaban makarantar ya ce, suna godiya da wannan nasara da suka samu a wannan karamin lokacin.

Daga cikin Malamai da suka gabatar da wa’azi a wajen taron akwai babban Darakta a sashin kula da lamuran addinai na jihar Kaduna wato Shiek Abubakar Jamilu Albani Samaru.


Shiek Albani Samaru ya yi nasiha ne ga 'yan’uwa musulmi baki daya kan muhimmancin daraja Al-kur’ani mai gima kuma ya jinjinawa wanda suka yi sauka da wanda suka yi hadda a wannan makarantar, ya kuma janyo hankalin musulmi wajen muhimmacin karanta Alkur’ani mai girma. 

Bayan gabatar da daliban masu sauka da masu hadda ne sai aka ba su damar yin karatu don masu saurare su tabbatar kuma su shaida da abin da suka zo doninsa. Daliban sun nuna bajintarsu a tsakiyar fili kuma a bainar jama’a.

An gudanar da neman taimako kuma bisa yadda hukumar makarantar ta nuna kokarinta yasa 'yan siyasa da 'yan kasuwa da jama’ar gari suka nuna soyayya ga hukumar makarantar wajen bayar da taimakon.


Zainab Idris na daya daga cikin daliban da suka sami shahadar yayin da take zantawa da manema labarai a wajen taron ta nuna jin dadinta da ta sami kanta cikin mahaddata a wannan lokacin don haka ta yi godiya ga malamai da iyayenta da suka ba ta damar samun wannan ilimin, a karshe ta mika sakon godiya ga duk wanda suka zo don taya su murna ta ce Allah ya mayar da kowa gida lafiya.


Zaharaddin Yusuf na daga cikin wanda suka sami shahada cikin maza shima godiya ya yi ga damar da Allah ya ba su a lokacin da matasa da yawa suke maida hankalinsu wajalen wasan kwallo su sai Allah ya maida na su wajen karatun Alkur’ani mai girma, ya ce suna godiya. A karshe ya yi fatan alheri ga iyaye da Malamai.

Tsohon Kakakin Majalisar jihar Kaduna, Abdullahi Shagali

Shi ko shugaban sashin gudanar da jarabawa na makarantar Malam Shuaib Shehu ya yi kira ne ga daliban da su yi koyi da Sahabban Manzon Allah wajen riko da littafin Allah kuma ya yi kira gare su su zama jakadu na kwarai kamar yadda aka ba su tarbiya, ya yi kira ga iyaye da su kara kaimi wajen bai wa yara kwarin guiwar zuwa makaranta a kan lokaci.

A wannan karon bincike ya nuna cewa akalla makarantar ta yi nasarar gina azuzuwa 14, ofishi guda 4, makewayi guda 7, shaguna 6 da makeken fili guda 1.
Kuma makarantar na da bangaren matan aure da bangaren maza a sashin Islamiyya.

Bugu da kari binciken ya tabbatar mana da cewa a wannan karo makarantar ta sami a kalla dalibai guda 85 a bangaren Hadda da bangaren sauka 33 maza 52 mata .

Daga cikin manyan bakin da suka sami halartar wannan waje akwai tsohon Kakakin majalisar jihar Kaduna Honorabul Aminu Shagali, sai Honorabul Bashir Sakadadi, akwai Honorabul Ali Baba, Shiek Albani Samaru da wakilan makarantu da shugabanin cibiyoyin ilmi dake Zariya. 

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments