Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masu Tallafawa: Tsakanin Gwarzo Da Agaka - Fassarar Ali Kakaki

Daga Yushau A. Shuaib  Fassarar Ali Kakaki Ba su da ra'ayin siyasa, ba su da bangaranci amma duk da haka suna bayar da gudummawa ga ci...



Daga Yushau A. Shuaib 

Fassarar Ali Kakaki

Ba su da ra'ayin siyasa, ba su da bangaranci amma duk da haka suna bayar da gudummawa ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki ta hanyar samar da ayyukan da suka dace, shirye-shiryen tallafawa da kuma tallafin karatu.

A matsayinsu na masu taimakon al’umma, Farfesa Abubakar Adamu Gwarzo da Injiniya Kale Kawu Agaka, sun nuna cewa bada mukamin siyasa kawai ba, mutum na iya yin kyakkyawan tasiri ta hanyar samar da ayyukan ci gaba a al’ummarsa da ma kasa baki daya.

A lokuta daban-daban a kuma taruka mabambanta, na ci karo da mutanen nan biyu na ƙarnin X kuma na lura da dimbin kuzari da arzikin da suka yi amfani da shi wajen tabbatar da ci gaban al'umma.

Gwarzo, hamshakin dan kasuwa na duniya, Farfesa ne a fannin Harsunan zamani na Turawa (Faransanci), kuma shi ne wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha ta Nijeriya (MAAUN), ya zuba dimbin jari sosai a manyan makarantun kasar nan domin tabbatar da samar da ilimi mai inganci a kasar nan.

Agaka, Injiniyar lantarki kuma Darakta a hukumar samar da wutar lantarki ta yankunan Karkara (REA), ya tabbatar tare da kuma kula da samar da ingantattun na’urorin wutar lantarki a al’ummomi daban-daban a fadin Nijeriya.

Kasa da shekara guda da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta bayar da lasisin gudanar da aikin Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) a harabarta ta Kano, wato a ranar Litinin 15 ga Fabarairu, 2021, Farfesa Gwarzo har ya gina hanyoyi masu nagarta a yankin, titin masu tafiya a kafa, tare da koriyar ciyawa da kuma shimfida kyakkyawan furanni. Ya zuwa watan Maris din wannan shekara, har ya riga da ya kammala kyawawan gine-gine, kamar gine-ginen Tsangayoyin karatu, dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje, gidajen ma’aikata, wajen cin abinci, wajen wasanni, da dai sauransu, a cikin birnin Kano.

Duk da kasancewarsa daya daga cikin mafi kyawun jami'o'i masu zaman kansu a arewacin Nijeriya a yau, wanda ya kirkiro Jami’ar ya yi kokarin saukaka kudin karatun daliban da ke karatun digiri a kasa da N1,000,000 (naira miliyan daya) a kowanne zangon karatu. Darussan da aka amince da su domin fara karatunsu a cikin Jami'ar suna Æ™arÆ™ashin Makarantun Gudanarwa (Schools of Management), Kwamfuta da Doka (Computing and Law). Sannan kuma akwai Makarantar Kimiyyar Kiwon Lafiya, wacce É—alibai za su iya karatun Unguwanzoma (Nursing), Kimiyyar gwaje-gwajen lafiya (Medical Laboratory Science) da kuma lafiyar jiki (Physiotherapy).

Gami da karawa bisa ga abubuwan da ake da su masu nagarta a Jami’ar, ta hanyar shirinsa na taimakon jama’a, AAG-Foundation, Farfesa Gwarzo ya ba da gudummawar motoci da motocin daukar marasa lafiya ga wadansu zababbun manyan makarantun ilimi a Arewa maso yammacin Nijeriya. Har ila yau, Gidauniyar tana jagorantar kamfen domin inganta hanyar samun ingantaccen ilimi, Æ™arfafa tsarin kiwon lafiya, zaburar da mata da matasa domin haɓɓaka daidaiton jinsi.

Dan kasuwar, wanda ke gudanar da wata Jami’a irin tsarin ta Amurka a Jamhuriyar Nijar, ya yi alkawarin kafa Jami’ar Franco British International University a Kaduna da kuma Jami’ar Canada a Abuja nan ba da jimawa ba.

A yayin da ’yan kasuwa da dama suka gwammace su saka hannun jari a kasuwancin gidaje da sauran sana’o’i masu tarin yawa, abin a yaba ne sosai ganin yadda Farfesa Gwarzo ke zuba jari mai yawa a fannin ilimi domin magance tabarbarewar ilimi da kalubalen da muke fuskanta a kasar nan, musamman a Arewacin Nijeriya.

Kazalika, Injiniya Kawu Agaka, Basaraken Masarautar Ilorin, a madadin Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara (REA) inda yake rike da mukamin Daraktan ayyuka, yana lura tare da kula da samar da Tiransifomar wutar lantarki masu inganci, fitillun dake amfani da hasken rana da kuma kananan tasoshin hasken lantarki, a kokarin ingantawa tare da tabbatar da tsayuwar hanyar samar da wutar lantarki a sassa daban-daban na kasar nan.

Baya ga samar da ci gaban ababen more rayuwa ta tsawo da fadin Nijeriya, Kawu Agaka, wanda a kwanakin baya Sarki Sulu Gambari ya nada shi a matsayin Dan-Iyan Masarautar Ilorin, yana ba da tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin garin da kuma shirye-shiryen koyon sana’o’i domin karfafawa matasa hanyoyin dogaro da kai, tare da tallafa wa Zawarawa da marayu da magunguna kyauta ta hanyar gidauniyar iyalansa.

Don haka ba abin mamaki ba ne yadda jama’a daga nesa da kusa da ba a taba ganin irinsa ba suka yi cincirindo a Fadar Sarkin da ke Ilorin a lokacin bikin nadin sarautar Dan-Iya. A haÆ™iÆ™a, da yawa daga cikin waÉ—anda suka ci gajiyar taimakonsa da sauran karamcinsa sun taka rawar gani a cikin wannan bikin Sarauta ta gargajiya ta hanyar ba da gudummawa mai yawa wajen gudanar da taron.

Sarautar Dan-Iya yawanci ana yi wa Basarake ne mai gaskiya da hangen nesa kuma wanda ke bada gudummawa ga al'ummarsa. Ana kuma ganin Agaka a matsayin wanda ya dace da wannan mukami, wanda mahaifinsa, Marigayi Alhaji Ibrahim Kawu Agaka, Basarake ne kuma hamshakin dan kasuwa, wanda ya kasance mutum na farko da ya fara rike mukamin.

Injiniya Agaka ya tabbatar da gaskiyar cewa ma’aikatun gwamnati, a matsayin babban hanyar hidima, ya kamata a yi amfani da shi wajen amfanar jama’a, domin ci gaban al’umma da ma kasa baki daya, ba don wata boyayyiyar manufa ba ko son rai ba. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara ya tabbatar da haka a lokacin da ya bayyana sabon Dan Iyan a matsayin abin alfaharin masarautar Ilorin.

AbdulRazaq ya ce a gaskiya wannan karramawar ta Sarautar gargajiya ta dace sosai da wanda aka bai wa saboda kyawawan dabi’un wanda aka karrama, da kaunarsa ga al’adun Ilorin da kuma yadda yake sadaukarwa wajen tallafawa al’umma.

“Zabensa a matsayinsa wanda za a bai wa wannan babban matsayi na Sarautar al’ada ya tabbatar da dimbin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’ummarmu, da goyon bayansa ga al’adunmu, da manufofinsa na bude kofa da kuma goyon baya, musamman ga matasa. Lallai mu muna alfahari da shi. Ina godiya ga Mai Martaba Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari, da majalisar Masarautar bisa kyakkyawan zabar mutumin kirki a matsayin Dan Iyan Geri (Ilorin),” in ji Gwamnan.

A cikin ayyukanmu masu ma'ana da kuma suka, ya kamata mu kuma yi Æ™oÆ™ari a koyaushe mu taya waÉ—anda ke ba da gudummawa ga ci gaban rayuwar al'umma. Farfesa Adamu Gwarzo da Injiniya Kale Agaka, a cikin É—imbin sauran jama’a, su ne abin koyi waÉ—anda ya kamata gudunmawarsu ta zaburar da wasu domin kwaikwayonsu, idan ba don ’yan Adamtaka ba, ta hanyar sadaukar da kai, sadaukarwa, da jajircewa wajen ganin an samu ingantacciyar al'umma, wacce za ta habbaka buÆ™atun ci gaban É—an adam.

A yayin da nake ba wanda ya kafa Jami’ar Amurka da ke Kano, Farfesa Gwarzo shawara da ya tabbatar da daukar kwararrun masana da gogaggun Malamai domin karantar da darussan ilimi, kazalika zan kuma bukaci Injiniya Agaka ya ci gaba da rike matsayinsa na siyasa, tare da tabbatar da daidaito da adalci wajen sauke nauyin da aka dora masa na ayyukansa da kuma ci gaba da ayyukansa na cikin al'umma ba tare da kyashi ba. Allah yasa dukkanin waÉ—annan mazajen biyu masu kirki su ci gaba da samun nasara, gamsuwa da kuma kwarin guiwar yin fiye da abin da suke yi a yanzu, a yayin da suke ci gaba da kawata mafi kyawun abin da É—an adam yakamata ya bayar.

Shu’aib, kwararren mai kula da harkokin yada labarai ne ya rubuto daga Abuja. www.YAShuaib.com


No comments