Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NATO Ta Ce Yakin Rasha Da Ukraine Ba Nata Ba Ne

  Rfi ta labarto cewa; babban Sakataren kungiyar tsaro ta   NATO Jens Stoltenberg ya ce kungiyar ba za ta kakaba dokar hana zirga-zirgar jir...

 


Rfi ta labarto cewa; babban Sakataren kungiyar tsaro ta  NATO Jens Stoltenberg ya ce kungiyar ba za ta kakaba dokar hana zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyar Ukraine ba, biyo bayan kiraye kirayen da mahukuntar kasar ke yi na taimakawa wajen taka wa Rasha birki a kan luguden wuta da take yi a kan kasar.

A yayin wani  taron gaggawa na ministocin harkokin waje na kasashen NATO, Stoltenberg ya ce  hanya daya tilo da za  a bi wajen aiwatar da dokar hana zirga zirgar jiragen sama a Ukraine ita ce ta harbo jiragen saman Rasha, kuma yin haka zai kai ga babban yaki a Turai, wanda zai shafi kasashe da dama.

Stoltenberg ya yi kashedin cewa al’amura na iya rincabewa fiye da yadda ake gani a yanzu a  kwanaki masu zuwa, inda za a samu karin asarar rai da wahalhalu da barnace barnace, duba da yadda Rasha ke shigowa da manyan makamai tare da ci gaba da hare hare a fadin kasar.

NATO, wadda ta ce wannan yaki ba nata bane, ta dau wannan mataki ne duk da magiyar da  shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke yi ta a taimaka masa wajen dakatar da luguden wutar da Rasha ke yi a biranen  kasarsa.

Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya gabatar da jawabi ga taron ta kafar bidiyo, inda ya mika bukatar daukar mataki kafin a makara, yana mai cewa a shirye suke su kare kansu, amma suna neman taimako.

No comments