Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya ta kasa samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da kasar Qatar za ta karbi bakunci a wannan ...
Tawagar ‘yan wasan
Super Eagles ta Nijeriya ta kasa samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da
kasar Qatar za ta karbi bakunci a wannan shekarar.
Nijeriya ta kasa samun
tikitin ne bayan tashi wasa 1-1 da tawagar kasar Ghana a wasan da suka fafata a
filin wasa na Moshood Abiola dake babban birnin Tarayya Abuja.
A wasan farko dai da
suka fafata a birnin Kumasi na Ghana kasashen biyu sun tashi wasa babu ci yayin
da aka tashi 1-1 a wasan da suka fafata a daren jiya.
Da wannan sakamakon,
kasar Ghana ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya inda za a zama daga
cikin wadanda za su wakilci Afirka.
Nijeriya dai ta samu
nasarar zuwa gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Russia a shekarar dubu
biyu da sha takwas.
No comments