Daga Wakilinmu Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bada umarnin raba kayan abinci ga mabukata don fara azumin R...
Daga Wakilinmu
Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bada umarnin raba kayan abinci ga mabukata don fara azumin Ramadan kamar yadda ya saba a duk shekara.
A yau Laraba Ofishin Jagoran ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa; "Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bada umarnin raba kayan abinci ga mabukata a matsayin tallafi don fara azumin watan Ramadan na wannan shekara ta 2022", ya labarta.
Idan ba ku manta ba, kamar yadda ya saba a duk shekara a lokaci irin wannan na Ramadana, jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky na raba kayan abinci ga mabukata a duk lokacin da watan Ramadana ya gabato. Kayan abincin sukan hada da shinkafa, Masara, Gero, Suga, Taliya da dai sauran su wanda akan isar da su ga mabukata.
MADOGARA ta labarto cewa; a shekarun baya ma a lokacin da Shehin Malamin ke daure a hannun gwamnatin Nijeriya tun bayan auka masa da gwamnatin ta yi a ranar 12 ga watan 12 na shekarar 2015, inda aka yi wa mabiyansa da 'ya'yansa kisan kiyashi, ya ci gaba da bai wa 'yan'uwansa na jini da wasu ba'adin almajiransa umurnin ci gaba da bai wa duk wadanda aka san yana bai wa wannan tallafi a lokacin da yake nan a duk Unguwannin Zariya da ma makwabta.
Wakilinmu ya labarto mana cewa; al'ummar da suka amfana da wannan tallafi sun yi matukar godiya bisa wannan karamcin da Shehin Malamin yake nuna musu.
Wata majiya ta labarta mana cewa; Shehin Malamin ya kwashe fiye da shekaru 20 yana irin wannan rabon a duk lokacin azumin watan Ramadana.
No comments