Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Shari'ar Rike Fasfon Shaikh Zakzaky: Kotu Ta Ja Kunnen DSS Da NIA

Daga Wakilinmu   Mai Shari'a Justice Obiora Egwuatu ya bada umurnin a kai ma hukumomin DSS da NIA takardar lallai su hallara...


Daga Wakilinmu 

Mai Shari'a Justice Obiora Egwuatu ya bada umurnin a kai ma hukumomin DSS da NIA takardar lallai su hallara a Kotu zuwa ranar 18 ga watan Mayu domin ci gaba da shari'ar.

Majiyarmu ta tattaro cewa kamar yadda aka É—auki tsawon lokaci ana gudanar da shari'ar Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky Da Mai ÆŠakinsa Malama Zeenah Ibrahim wacce suka maka hukumar shige da fice na kasa wato Immigration kan su sabunta musu takardarsu ta fita kasashen waje wanda ya dauki tsawon lokaci amma abun ya ci tura.

A zaman baya da aka gudanar a Babban kotun ƙasa dake Maitama, Abuja, Lauyan Hukumar hukumar shige da fice Barista Ustaz Jamil ya roƙi kotu da ta amince a shigo da hukumar tsaro da DSS cikin shari'ar sannan a shigo da Hukumar NIA, wanda bukatar hakan tasa Lauyoyin Shaikh Zakzaky suka ce ba su amince ba domin lamarin zai yi ta jan ƙafa duba da waɗanda ake magana a kansu ba su da lafiya a cewar lauyoyin.

Hakan ta sa Alƙalin dage shari'ar zuwa yau Litinin 28 ga watan Maris din 2022, inda aka zauna a yau, bayan zaman kuma Mai shari'a Justice Obiora Egwuatu ya bada umurnin a kai ma hukumomin DSS da NIA takardar lallai su hallara a Kotu zuwa ranar 18 ga watan Mayu domin ci gaba da shari'ar.

Mun nemi jin ta bakin ɓangaren Lauyoyin Malam Zakzaky domin jin yadda suka ji da hukuncin da kuma matakin da za su ɗauka kafin ranar amma abim ya ci tura haka ma bangaren Lauyoyin Hukumar shige da fice har zuwa haɗa Rahoton bamu ji komai ba.

No comments