Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sheikh Ibrahim El- Zakzaky: 'Watarana Zan Sake Koma Wa Zariya'

Rahoton BBC Hausa Shugaban Harkar Musulunci ta ƴan uwan Musulmai ta Mazahabar Shi'a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce yana da ...


Rahoton BBC Hausa

Shugaban Harkar Musulunci ta ƴan uwan Musulmai ta Mazahabar Shi'a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce yana da fata da burin koma wa Zariya a nan gaba don ci gaba da ayyukansa da yake yi a baya, musamman idan ya samu lafiyar jikinsa.

Sheikh Ibrahim Elzakzaky ya bayyana hakan ne a hirarsa ta farko da ya yi da wata kafar yaɗa labarai ta Hausa tun bayan da aka sako shi.

Fiye da shekara shida kenan tun bayan rikici tsakanin mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da sojojin Najeriya, bisa zargin da sojoji suka yi na cewa mabiya El-Zakzaki sun tare musu hanya a Zaria.

Ɓangaren Sheikh Zakzakin dai ya sha musanta batun tare hanyar inda suke cewa gwamnati ta yi amfani da hakan ne domin far musu a 2015.

Ƙungiyar Amnesty International ta ce wutar da sojoji suka buɗe kan mabiyan Zakzaky ta yi sanadin mutuwar mutum 345 a lokacin.

A watan Yulin 2021 kuma, wata babbar kotu a Kaduna ta wanke Sheikh Zakzaky da mai ɗakinsa daga dukkan tuhume-tuhumen da aka yi musu inda kuma aka sake shi bayan kwashe kimanin shekara shida a tsare.

Ga dai tsakure daga yadda hirar tasa ta kasance da shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko. Za mu kawo muku cikakkiyar hirar a ranar Asabar.

Sheikh Zakzaky ya fara ne da shaida wa Aliyu Tanko halin da yake ciki a yanzu.

Sheikh Zakzaky: Ɗaukata ake yi tun da an dagargaza min cinya ta dama, ba wai an karya ba an dagargaza min ita, haka hannuna ma na hagu an dagargaza shi.

Aliyu Tanko: Kamar harashi nawa kake tunanin an maka a hannun da ƙafar?

Sheikh Zakzaky: Ai harbe-harbe ne. Wato mutane ne suka tsuguna su huɗu suna ruwan harsasai a cikin ɗan ƙaramin ɗaki da muke.

Aliyu Tanko: Kai ka gan su?

Sheikh Zakzaky: E na gan su mana, gaba da gaba ma suna ɗora harsashi.

Aliyu Tanko: Wasu rahotanni da muka samu sun ce watakila ka ƙi yarda a tafi da kai ne?

Sheikh Zakzaky: A'a sun dai buɗe wutarsu ne kawai. Ai suna cewa cire kayan nan ta ce ba zan cire ba sai suka ce faya kawai, dama sun zo kisan kai ne. Sun kuma kashe ɗaruruwan mutane kafin su zo kanmu ai.

Sun ƙona gidan ƙurmus sun ɗauka mun ƙone ƙurmus ɗin ne.

Aliyu Tanko: A lokacin ka yi fargabar cewa wataƙila kai ma za su kashe ka?

Sheikh Zakzaky: Allah Ya sauwaƙe na yi fargaba. Akwai wanda ya ce min ko zan sauya muhalli na ce Allah Ya sauwaƙe, ba yadda za a yi an zo kashe ni kuma na tafi wani waje bayan kuma an kashe mutane kafin kaina.

Saboda haka su zo su cimma burinsu illa iyaka kenan su kashe ni, ina jiran kisan ne ba wani abu ba.

Wannan umarni ne, shi shugaban ƙasa shi da kansa ne ya ba da umarnin hakan daga Kaduna. Sai da aka ba shi tabbacin an ƙona gidana da ni da matata da ƴaƴana.

Aliyu Tanko: Wato zargin da kuke shugaban ƙasa ne ya sa aka yi hakan?

Sheikh Zakzaky: Ba zargi ba ne abin da ya faru kenan, kuma ai ya yi magana da aka tambaye shi ya ce Zakzaky ya yi gwamnati ne a cikin gwamnati.

Me wannan kalma ke nufi? Ka ga ya nuna cewa laifin Zakzaky ne, a ganinsa shi ke da gwamnati ga kuma Zakzaky yana da gwamnati don haka zai rusa gwamnatin Zakzaky, ya wuce haka nan.

Aliyu Tanko: Da za ka hadu da Buhari da Gwamna Nasiru El-Rufa'i na Kaduna me za ka ce musu?

Sheikh Zakzaky: Zan ce musu su kammala ayyukan da suka fara, su ci gaba su cikata ladansu.

Aliyu Tanko: Kamar me kenan?

Sheikh Zakzaky: Ba suna so su kashe ni ba ne, to ga fili ga mai doki.

Aliyu Tanko: Ba za ka nemi jin dalilansu na yin wadancan abubuwan ba?

Sheikh Zakzaky: Ai na sani. Mulki ne dai iyakarsa nan duniya ne, kwana nawa ne mulkin ai zai zo ya ƙare. Ita ma rayuwar za ta zo ta ƙare. a i lokacin da aka harbe ni wani minista cikin ministocin Buharin ya bugo min waya, na amsa an harbe ni ina kwance.

Na ce masa ka ga abin da gwamnatinku ta yi min ko? Na ce masa ka ce ina gaida Janar Buhari, ku yi gwamnati lafiya, sai mun haɗu a lahira.

Duk abin da za ku yi ku yi za mu tsaya a gaban Allah ranar gobe ƙiyama. Kuma ƙiyamar ba nisa gare ta ba.

Aliyu Tanko: Lokacin da abubuwa suka faru a Zariya, shin nan gaba Malam na tunanin koma wa Zariya ya gina muhallinsa da makarantarsa da sauran su?

Sheikh Zakzaky: In shaa Allahu ba abin da zai hana wannan. Amma da yake yanzu abin da yake gabanmu shi ne lafiyar jikinmu, amma in shaa Allah duk abin da muka rasa a Zariya za mu mayar da su kuma duk abin da ake yi za a ci gaba da yi.

No comments