Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shinkafi Ya Janye Takararsa Ta Neman Shugabancin Jam'iyyar APC Ta Ƙasa

Daga Hussaini Ibrahim Dan takarar Shugabancin Jam'iyyar APC ta ƙasa ,Alhaji Sani Abdullahi Wanbam Shinkafi ya bayyana janyew...


Daga Hussaini Ibrahim

Dan takarar Shugabancin Jam'iyyar APC ta ƙasa ,Alhaji Sani Abdullahi Wanbam Shinkafi ya bayyana janyewarsa daga takarar shugabancin Jam'iyyar saboda biyayya ga shugaban kasa da Uwar Jam'iyyar.

Shinkafi ya bayyana hakan ne a taron da ya yi da manema labarai a Gusau babban Birnin jihar Zamfara.

Dan takarar shugaban Jam'iyyar, ya kara da cewa, ya ayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin Jam'iyyar ne a ranar 17 ga watan Oktobar 2021. Sai kuma na tabbatar ma Uwar Jam'iyyar APC ta kasa , a ranar 22/1/2022 kuma a yau 21/3/2022; "Ina shaida ma ku cewa, na janye takarata ta shugabancin Jam'iyyar saboda ni mai biyayya ne ga shugaban kasa da Jam'iyyar akan sun yanke shawara wannan mukamin na shugabancin Jam'iyyar a barma Arewa ta Tsakiya shugabancin Jamiyyar. Don haka ni na bi wannan hukunci", inji Wanbam Shinkafi Sani Abdullahi.

Wanbam Shinkafi ya kuma mika godiyarsasa ga Kodinoninsa na jihohin kasarnan da Gwamnoni da magoya bayansa da dai sauransu.

Kuma ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Bello Matawalle da kuma gwamnan Borno da dai sauran su a cikin wannan tafiya ta.

No comments