Daily Trust ta labarto cewa; tsohon Gwamnan Jihar Legas, kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya s...
Daily Trust ta labarto cewa; tsohon Gwamnan Jihar Legas, kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya sanar da soke bikin ranar zagayowar haihuwarsa saboda harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Da yammacin ranar Litinin ne jirgin kasan ya taka wani bam da ’yan bindiga suka binne a titin jirgin, sannan suka kashe fasinjoji, kuma suka gudu da wasu da dama.
An dai tsara gudanar da bikin ne ranar Talata saboda taya shi murnar cika shekara 70 a duniya.
A maimakon haka, Tinubu ya bukaci malamai da sauran ’yan Nijeriya da su yi wa Nijeriya addu’ar ganin bayan ta’addanci.
Ya ce a matsayinsa na babba a kasa, bai dace ya gudanar da biki a daidai lokacin da wasu suke cikin alhini ba.
Tinubu ya bukaci dukkan mahalarta taron da su koma gida su yi wa Nijeriya addu’a
No comments