* Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da harin ƴan ta'adda a kan jirgin ƙasan Abuja Zuwa Kaduna Rahotannin dake shigo mana a halin...
*Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da harin ƴan ta'adda a kan jirgin ƙasan Abuja Zuwa Kaduna
Rahotannin dake shigo mana a halin yanzu daga wata majiya ta labarta mana cewa; tsohon mataimakin Gwamnan jihar Zamfara Malam Ibrahim wallafa na daga waɗanda suka samu raunin Harbin bindiga a harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a daren Jiya.
Gwamnatin jihar Kaduna a ta janibinta ta tabbatar da harin da ƴan ta'adda su ka kai a kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a yammacin jiya Litinin.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ƴan ta'addan sun tashi bam a kan layin dogo na jirgin ƙasan Abuja-Kaduna, inda su ka samu nasarar tsayar da jirgin cak a wani waje tsakanin Katari da Rijana.
A wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar, gwamnatin jihar ta samu rahoton harin ne da ga hukumomin tsaro.
A cewarsa, gwamnatin na samun rahoton, sai ta tuntuɓi hukumomin da su ke da alhaki, inda kan ka ce kobo, su ka isa wajen domin tserar da fasinjojin cikin jirgin.
Tuni dai a ka kwashe fasinjojin da ga wajen, inda a ka garzaya da wadanda su ka samu raunuka zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Kaduna za ta haɗa gwiwa da hukumar sufurin jirgin ƙasa domin fitar da sunayen fasinjojin domin sanin cikakken bayanin su.
Gwamnan jihar, Nasir El-rufa'i, ya yaba wa jami'an tsaro bisa gaggawar kai ɗauki wajen da lamarin ya faru, inda ya gode musu a bisa ƙoƙarin su na kare jirgin da kuma tserar da fasinjojin.
No comments