Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Matan Shugabannin Kananan Hukumomi Sun Ziyarci Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna

Daga Idris Umar Kaduna Ƙungiyar matan shugabannin Kananan hukumomi na jihar Kaduna sun ziyarci Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna...


Daga Idris Umar Kaduna

Ƙungiyar matan shugabannin Kananan hukumomi na jihar Kaduna sun ziyarci Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa.

Uwargidan shugaban Ƙungiyar kananan Hukumomin jihar Kaduna ALGON ne ta jagoranci tafiyar ta su. 


Kamar yadda shugaban kungiyar kuma matar shugaban ALGON, Honorabul Liman Abubakar Buba ta sanar cewa wannan ziyara ta kumshi ta sada zumunci ne da neman goyan baya ga ƙungiyar matan shugabannin kananan hukumomi na jihar Kaduna, haka zalika matan sun roki arzikin karfafa harkokin mata da matasa a jihar ta su baki daya kamar yadda mataimakiyar gwamnan ta wallafa a shafinta na Facebook.

No comments