Daga Aisha Suleman Zariya Ƙungiyar manyan ma'aikata da kanana na Jami'o'i sun garzaya yajin aikin gargadi ga Gwamnat...
Daga Aisha Suleman Zariya
Ƙungiyar manyan ma'aikata da kanana na Jami'o'i sun garzaya yajin aikin gargadi ga Gwamnatin Tarayya. Wakilinmu ya ziyarci ofishinsu kungiyoyin na ƙasa reshen Jami'ar Ahmadu Bello Zariya don ji da ganin yadda lamarin zai wakana a yau 28/3/2022.
Tuni gamayyar ƙungiyoyin 2 wato SSANU da NASU suka mamaye harabar babban benen harkar mulki na jami'ar wato 'Senate Building' dake harabar jami'ar tare da hana duk wani ma'aikaci shiga ciki.
Gamayyar ƙungiyoyin sun rika rera wakoki dake nuni da babu gudu babu ja baya wajen fafutika da suka fara a fadin ƙasar baki daya.
Bayan sun gudanar da kwarya-kwaryar mitin ne wakilinmu ya zanta da shugaban ƙungiyar ta SSANU Kwamared Muhammed A Yunusa ya ce suna biyayya ne ga Uwar kungiyarsu ta ƙasa akan tafiyarsu yajin aiki bisa rashin cika masu alƙawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi musu.
Shugaban ya kara da cewa, za su ci gaba da yajin aiki har na tsawon sati biyu a matsayin yajin aikin gargadi. Kuma shugaban ya yi kira ga gwamnati cewa ya kamata ta tausayawa 'ya'yan ƙungiyar bisa ga yadda suke bada gudummawarsu a bangarori da dama musamman harkar ilimi da sauransu.
Ƙarshe ya yi kira ga 'ya'yan ƙungiyar da su bi doka da oda yayin gudanar da yajin aikin. Ya cewa 'ya'yan ƙungiyar "ku zauna a gida sai Uwar ƙungiyar ta kira ku kar ku zo aiki".
Shima takwaransa shugaban ƙungiyar kananan ma'aikatan Jami'ar ta Ahmadu Bellon Zariya wato NASU Kwamared Muhammed Sunusi Garba shima cewa ya yi suna nan akan bakansu na zuwa yajin aiki bisa biyayya ga Uwar kungiyarsu ta ƙasa baki daya.
Ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta zama mai cika alkawari don ci gaban ƙasa baki daya.
Shima ya yi kira ga 'ya'yan ƙungiyar ta su da su zama masu bin doka wajen fafutikar nemawa juna 'yanci don haka ya ce kowa ya zauna a gida sai an kira shi kamar yadda aka saba har tsawon sati biyu.
Kwamared Sunusi ya yi fatan gwamnati za ta zama mai tausayawa kuma ya tabbatar da cewa za su tafi yajin aikin har na tsawon sati biyu karkashin wasikarsu mai lamba JAC/NS/VOL 192 ta 16/3/2022 da aka aikewa ministan kwadago na kasa.
Ya zuwa hada wannan rahoto komi ya tsaya cak a cikin Jami'ar ba dalibai ba ma'aikata sai masu gadi.
Sai kasidu da gamaiyar ƙungiyoyin suke rabawa mai dauke da sa hannun babban Sakataren NASU Prince Peters A Adeyemi. Da na shugaban ƙungiyar SSANU ta ƙasa Kwamared Muhammad H. Ibrahim.
No comments