Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Wane Ne Sadaukin Zazzau Malam Yusuf Shehu Idris?

Daga Idris Umar Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai. A yau tabaranmu zai hasko mana daya daga cikin 'ya'yan Sarki ne m...


Daga Idris Umar

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai. A yau tabaranmu zai hasko mana daya daga cikin 'ya'yan Sarki ne mai tausayi da son ya kamata, ba kowa bane face Sadaukin Zazzau. To amma wane ne Sadaukin Zazzau?

Sadaukin Zazzau na ɗaya daga cikin Sarautu da aka aro daga Daura a lokacin mulkin Fulani, zamanin Mulkin Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, wanda aka fara naɗawa shi ne Malam Yusuf Shehu Idris.

Sadaukin farko a Masarautar Zazzau shi ne Malam Yusuf Shehu Idris, ɗan Sarkin Zazzau Shehu Idris, ɗan mai Unguwa Idris Auta, ɗan Sarkin Zazzau Mallam Sambo, ɗan Sarkin Zazzau Mallam Abdulkarim Sarki na farko a gidan Sarautar Katsinawa, to ka ga Sadaukin Zazzau ɗan na gada ne ba ɗan na haya ba. Sadaukin Zazzau Malam Yusuf Shehu Mutum wanda ya rike Sarauta yadda ya kamata, Saboda irin yadda ya rike Sarautar Sadaukin gaba ɗaya ya ƙara fito da Sarautar Sadaukin a Daular Usmaniyya. 

Tun bayan da aka naɗa shi Sadaukin Zazzau da yawan Masarautu da muke da su a Arewacin Nijeriya sai da suka naɗa Sarautar Sadauki. Duk cikin Masarautun da ke daular Usmaniyya ban san wani matashin Basarake ɗan Sarkin da ya rike hidimar Manzon Allah (S.A.W) kamar Mai Girma Sadaukin Zazzau Malam Yusuf Shehu Idris, duk in da ka ga ana hidimar Annabi Muhammadu (S.A.W)  to za ka ga Mai Girma Sadauki da tawagarshi, domin shi ɗin masoyin Annabi ne na haƙiƙa. 

Duk wata hidima in dai aka ce mai na Annabi ne to ba ya kasa a gwiwa wurin ganin ya halarta, kar ku ce wai a Masarautar Zazzau ne kaɗai yake zuwa hidimar Annabi a ko'ina a faɗin duniya, indai maganar Manzon Allah (S.A.W), ka gayyace shi, in Allah ya yarda za ka ga Mai Girma Sadauki a wurin, muna Addu'ar Allah ya ƙara mana son Manzo Allah (S.A.W).

Haka kuma Mai Girma Sadaukin Zazzau Malam Yusuf Shehu Idris na ɗaya daga cikin 'ya'yan Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Shehu Idris, wanda da ka ji muryar shi ka san wannan jini ne na Sarkin Zazzau Shehu Idris, haka kuma iya ƙwalliya da  ado duk lokacin da zaka gan shi zaka ganshi ne a shiga irin na Sarauta hakan zai sa ka san wannan jinin sarauta ne ba sai an faɗa maka ba, ɗan Sarkin Shehu Waliyin Allah ne, saboda shima ya yi gado irin wannan ƙwalliyar ta Balaraben Sarakuna Autan Sambo, Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Dr Shehu Idris.

Wannan duk kirarin mai girma Sadaukin Zazzau ne. Duk da irin gidan da Mai Girma Sadaukin Zazzau ya taso bai taɓa hana shi shiga kasuwanci ba don neman na kan shi, bai zauna ya dogara da cewa mahaifina yana da shi mai zai sa in wahalar da kai na ba, shiyasa ya tashi ya fara neman na kan shi,  don shi mutum ne ɗan kasuwa sosai,  don har gobe Mai Girma Sadaukin Zazzau yana kasuwanci, ga shi kuma manomi ne sosai, don ita ma Nomar har gobe yana yi,  haka kuma za ka ji yana ba matasa shawarar karku ce Sarauta da aikin gwamnati zaku tsaya ma, ku yi sana'a da kasuwanci, don Sarauta ba kudi baza ta taɓa tafiya daidai ba.

Mai Girma Sadaukin Zazzau mutum ne mai biyayya kamar yadda aka san 'ya'yan Sarki da biyayya, sannan shi mutum ne mai bin na gaba da shi, kuma kamar yadda aka san 'ya'yan Sarauta da rashin tsoro haka Mai Girma Sadaukin Zazzau mutum ne da bai san tsoro ba, gashi mai son zumunci da ƙaunar Jama'a. Allah ya ji ƙan Sarkin Zazzau Shehu Idris, yasa yana ƙyaƙƙyawan matsayi da duk Sauran al'ummar Musulumi baki ɗaya.


Muna Addu'ar Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, ya  ƙara girma da ɗaukaka, ya shirya maka zuri'a ya biya maka buƙatun ka na duniya da lahira, ya kare ka daga sharrin mahassadi da makiya a duk inda suke a duniyar nan, Ameeen ya Allah.

Kirarin Sadaukin Zazzau

Damin bakin Rumbu
Kosar da maigani
Saka musu sa musu
Dan Bajimin sarki
Dan Cigari Uban Gabasawa

Mai Girma Sadaukin Zazzau Malam Yusuf Shehu Idris ya yi karatun addini a Fadar Zazzau kuma ya yi karatun zamani tun daga Firamare har Jami'ar Ahmadu Bello University Zariya inda ya karanta 'Building Engineering' wato fannin Gine-gine na zamani har digiri na biyu wato Master of Information Management.

Mai Girma Sadaukin Zazzau Malam Yusuf Shehu Idris Allah ya azurta shi da zuri'a 'ya'ya har Biyar. 

Yanzu Haka ma'aikacin Gwamnatin Tarayya ne a Ma'aikata Horar da Malamai dake Kaduna wato National Teachers Institute (NTI ) Kaduna.

No comments