Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Yadda Bikin Bude Masallaci Ya Gudana A Garin Giwa Ta Jihar Kaduna

Daga Idris Umar Kaduna A cikin satin da ya gabata ne ne al'ummar karamar hukumar Giwa suka yi walimar bude masallacin a ciki...


Daga Idris Umar Kaduna

A cikin satin da ya gabata ne ne al'ummar karamar hukumar Giwa suka yi walimar bude masallacin a cikin garin Giwa ta jihar Kaduna. Wakilanmu sun shaida yadda walimar ta gudana.

Masallacin dai yana daya daga cikin masallatai masu kyau da tsari a fadin karamar hukumar ta Giwa.

Alhaji Aminu Idris Mai Kemis ne ya gina shi kuma ya zuba duk wani Abu da masallaci ke bukata.

Manyan Malamai ne da manyan 'yan siyasa harda Alkalai da shuwagabanin Cibiyoyi ne suka shaida yadda bukin bude masallacin ya gudana. Kuma dukkansu sun yi yabo ga shi Alhaji Aminu Mai Kemis da ya gina wannan Masallacin a matsayin sadakatul jariya.

Bayan bude masallaci ne wakilanmu suka samu zanta da wanda ya gina masallacin a takaice.

Malam Aminu ya ce; "abin da ya ja hankali na zuwa gina wannan Masallaci shi ne ina neman yardar Ubangiji ne ga dukkan al'amurana a duniya da lahira".

Karshe Alhaji Aminu Idris ya yi godiya ga dukkan Sarakuna da manyan Malamai da suka zo don sanya mishi albarka a wannan lokaci. Kuma ya yi fatan Allah ya mayar da kowa gida lafiya.


Daga cikin manyan baki da kuma manyan Malamai da suka shaida wannan walimar ta bude wannan masallacin akwai wakilin Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai wato Shiekh Abubakar Albani Samaru sai wakilin shugaban karamar hukumar Giwa da shugaban majalisar malamai na karamar hukumar Giwa da Honorabul Lawal Sa'ila Yakawasa da dai sauran manyan mutane da suka hada gida da wajen karamar hukumar ta Giwa da jihar Kaduna baki daya.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments