Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Rasha Ta Kai Hari Cibiyar Sarrafa Nukiliya Mafi Girma A Turai

  Dakarun Rasha sun kai hari kan tashar nukiliya mafi girma a Turai da safiyar yau Jumma’a, matakin da ya haifar da gobara a cibiyar dake ts...

 


Dakarun Rasha sun kai hari kan tashar nukiliya mafi girma a Turai da safiyar yau Jumma’a, matakin da ya haifar da gobara a cibiyar dake tsakaiyar  Ukraine, inda shugaban kasar ya zargi Moscow da "ta'addancin nukiliya".

Harin ya zo ne a daidai lokacin da sojojin Rasha suka kara kaimi wajen kai hare-hare a garuruwa da dama a kasar ta Ukraine da suka hada da Chernihiv da ke arewacin kasar, inda jami'ai suka ce fararen hula 33 ne suka mutu.

Tuni shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Moscow da "ta'addancin nukiliya" jim kadan bayan da sojojin Rasha suka kai hari cibiyar samar da wutar lantarki ta Zaporizhzhia, tashar nukiliya mafi girma a Turai, dake gabashin birnin Energodar.

Hukumomin yankin suka ce harin baiyi barna sosai ba, kuma gobarar ba ta shafi “mahimman” kayayyakin cibiyar Nukiliyar ba, ko da yake har yanzu ba a san abin da zai biyo baya ba.

Hukumar bada agajin gaggawa a yankin Chernihiv da ke gabashin kasar ta ce an ciro gawarwaki mutane 33 daga baraguzai bayan ruwan bama-bamai da dakarun Rasha suka kai ta sama, wanda gwamna Viacheslav Chaus ya ce harin ya shafi gidaje da makarantu biyu.

Yayin da take ci gaba da luguden wuta a bangare daya, Kasashen na Rasha da Ukraine sun amince da bukatar samar da hanyoyin jin kai domin kwashe fararen hula, tare da yiwuwar tsagaita wuta, kamar yadda babban mai shiga tsakani na Rasha Vladimir Medinsky ya bayyana bayan tattaunawa da Ukraine.

 

No comments