Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Yan Kungiyar NURTW Sun Kai Wa Hukumar Kashe Gobara Hari A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim Kungiyar ma’aikatan zirga-zirgar ababen hawa ta kasa, reshen jihar Zamfara wato NURTW ta kai wa ma’aikatan...Daga Hussaini Ibrahim

Kungiyar ma’aikatan zirga-zirgar ababen hawa ta kasa, reshen jihar Zamfara wato NURTW ta kai wa ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar hari, in da suka raunata shugaban hukumar da wasu ma’aikatansa goma .

Membobin Kungiyar NURTW reshen Jihar Zamfara, karkashin jagorancin Shugaban ta Namadi kasuwan Daji sun kai hari ga hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara, sakamakon wata 'yar hatsaniya da ta faru, bisa zargin daukar fasinja a bakin hanya.

Wasu jami'an kashe gobara sun samu munanan raunuka ciki harda Shugaban hukumar, Abdullahi Jibo Dauran, aka kuma kai su asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau babban birnin jihar domin samun kulawar gaggawa.

Da yake zantawa da manema labarai a lokacin da ya ke kan gadon Asibiti, Daraktan hukumar kashe gobara na jihar, Abdullahi Jibo Dauran, ya ce ‘yan kungiyar ta NURTW sun kai mamaya da motoci kirar Hummer guda uku cike da matasa, dauke da muggan makamai, tare da shugabansu Hamisu Kasuwar Daji inda ya umarce su da su kai wa jami’ansu hari nan take sai duka da sara da adduna da kuma jifa .

Abdullahi Jibo ya kara da cewa, yana kokarin shawo kan jami’ansa inda ya umurce su da su kulle kofarsu amma ‘yan kungiyar NURTW sun yi galaba a kansu inda suka fara dukansu da sanduna suka raunata mutane goma ciki har da ni kaina Daraktan hukumar.

A lokacin da Wakilinmu ya ziyarci ofishin hukumar kashe gobara ta jihar, ya gamu da daya daga cikin wanda aka fara takaddama da shi mai suna Lawali Damba inda ya ce, rikicin ya biyo bayan wata ‘yar karamar rashin jituwa da ta samu tsakaninsa da ‘yan kungiyar wanda aka sasanta cikin lumana, daga bisani kuma ya ta’azzara sakamakon shigowar shugabansu Hamisu Kasuwar Daji cikin lamarin.

Da yake bayyana matsayin gwamnati, Kwamishinan ayyukan Alhaji Rabiu Garba ya ce tuni ya mika wa mataimakin Gwamnan jihar Sanata Hassan Nasiha wanda kuma shi ne mukaddashin gwamna bayanan abin da ya faru dan daukar matakin gaggawa akai.

Ya kuma bayyana lamarin a matsayin na dabbanci, abin takaici ganin cewa a halin yanzu gwamnatin jihar na iya bakin kokarinta wajen ganin ‘yan kasa sun samu dawwamammen zaman lafiya a fadin jihar.

SP Muhammad Shehu shi ne jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta Jihar Zamfara ya tabbatar da faruwan lamarin ya kuma bayyana cewa, suna nan suna gudanar da bincike kan lamarin, kuma za su dauki matakin da ya dace.

No comments