YANZU-YANZU: Awa 24 Da Kai Wa Jirgin Ƙasa Hari, 'Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja


Rahotannin da ke shigo mana na nuni da cewa 'yan bindiga a yau Talata sun tare babbar hanyar zuwa Abuja zuwa Kaduna, inda suka yi garkuwa da mutane da dama awanni da kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja hari. 

Majiyarmu ta Jaridar SAHELIAN TIMES ta labarto cewa Kakakin 'yan sandan Nijeriya na Kaduna ba a same shi ba domin tabbatar da labarin. Amma wani ganau ya ce 'yan bindigar sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna da muggan makamai. 

Karin bayani zai zo daga baya. 

Post a Comment

0 Comments