Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

YANZU-YANZU: Sojoji Sun Hallara Inda 'Yan Bindiga Suka Tare Jirgin Kaduna Zuwa Abuja

Daya daga cikin fasinjojin dake cikin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya tabbatar da cewa Rundunar Sojin Nijeriya sun hallara ind...


Daya daga cikin fasinjojin dake cikin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya tabbatar da cewa Rundunar Sojin Nijeriya sun hallara inda 'yan bindiga suka tare jirgin kasan bayan da suka dasawa titin jirgin bom da ya tilastawa jirgin tsayawa. 

Anas Iro Danmusa daya daga cikin fasinjojin jirgin, ya tabbatar da cewa sojoji sun iso wurin bayan kwashe sama da awa daya da 'yan bindigar suka tare fasinjojin. 

Rahotanni a cikin n daren yau Litinin sun labarta cewa wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun dasa bom a titin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, inda suka tilasta dakatar da jirgin. 

Majiyarmu ta labarta mana cewa lamarin ya faru ne a tsakanin garin Katari zuwa Rijana a daren yau Litinin. 

Daya daga cikin fasinjojin wanda ya shaida lamarin ya ce: 'yan bindigar sun kuma zagaye jirgin inda suka bude wuta na kan mai uwa da wabi, inda fasinjojin suka kwanta a cikin jirgin. 

Daya daga cikin wanda suka san adadin fasinjojin dake jirgin, ya labartawa Majiyarmu cewa akwai akalla Fasinjoji 970 a jirgin. 

No comments